Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Faburairu 2027 › Faburairu 12

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Faburairu 12, 2027

Juma’a · Lokacin Azumi: kwanakin bayan Laraba ta Toka

Bukukuwa da waliyyai

Juma’a bayan Laraba ta Toka

Ranar mako · Launin ibada: shunayya

Azumi da tuba

Kamewa daga nama

Kowace Juma’a ranar tuba ce; kowace taron bishop-bishop yana tsara yadda ake kiyaye ta: kamewa daga nama ko wani aikin tuba. Azumi ya wajaba daga shekara 18 zuwa 59, kamewa daga shekara 14.

Karatun yini

Karatu na farko

Ish 58:1–9

1“Ku yi ihu da ƙarfi, ba ƙaƙƙautawa. Ku tā da muryarku kamar busar ƙaho. Ku furta wa mutanena tawayensu da kuma ga gidan Yaƙub zunubansu. 2Gama kowace rana suna nemana; suna marmarin sanin hanyoyina, sai ka ce al’ummar da take yin abin da yake daidai ba ta kuma yashe umarnan Allahnta ba. Sun nemi shawarwaran da suke daidai daga gare ni suna kuma marmari Allah ya zo kusa da su. 3Suna cewa, ‘Don me muka yi azumi, ba ka kuma gani ba? Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu, ba ka kuma lura da wannan ba?’ “Duk da haka a ranar azuminku, kuna yi yadda kuka ga dama kuna kuma zaluntar dukan ma’aikata. 4Azuminku yakan ƙare a faɗa da kuma hargitsi, kuna ta naushin juna da mugayen naushe-naushe. Ba za ku iya azumi kamar yadda kuke yi a yau ku zaci za a ji muryarku can sama. 5Irin azumin da na zaɓa ke nan, rana guda kawai don mutum ya ƙasƙantar da kansa? Sunkuyar da kanku kamar iwa kawai kuna kuma kwance a tsummoki da toka? Abin da kuke kira azumi ke nan rana yardajje ga Ubangiji? 6“Irin azumin da na zaɓa shi ne, a kunce sarƙoƙin rashin adalci a kuma kunce igiyoyin karkiya, a ’yantar da waɗanda ake zalunta a kuma kakkarye kowace karkiya? 7Ba shi ne ku rarraba abincinku da mayunwata ku kuma tanada wa matalauta masu yawo mahalli, sa’ad da kuka ga wanda yake tsirara, ku yi masa sutura, kada kuma ku ba wa namanku da jininku baya? 8Sa’an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir, warkarwarku kuma zai bayyana nan da nan; sa’an nan adalcinku zai tafi a gabanku, ɗaukakar Ubangiji kuma zai tsare ku daga baya. 9Sa’an nan za ku yi kira, Ubangiji kuma zai amsa; za ku yi kuka don neman taimako, zai kuwa ce ga ni nan. “In kuka kawar da karkiyar zalunci, kuka daina nuna wa juna yatsa da kuma faɗar mugayen maganganu,

Zaburar amsawa

Zab 51:1–4, 16–17

1Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da annabi Natan ya zo wurinsa bayan Dawuda ya yi zina da Batsheba. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa; bisa ga tausayinka mai girma ka shafe laifofina. 2Ka wanke dukan kurakuraina ka tsarkake ni daga zunubina. 3Gama ina sane da laifofina zunubaina kuma kullum suna a gabana. 4Kai kaɗai na yi wa zunubi na yi abin da yake mugu a idonka, ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta. 16Ba ka farin ciki a hadaya, ai da na kawo; ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa. 17Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu; karyayyiya da kuma zuciya mai tuba, Ya Allah, ba za ka ƙi ba.

Bishara

Mat 9:14–15

14Sai almajiran Yohanna suka zo suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa mu da Farisiyawa muke azumi, amma almajiranka ba sa yi?” 15Yesu ya amsa ya ce, “Yaya baƙin ango za su yi makoki yayinda yake tare da su? Lokaci yana zuwa da za a ɗauke ango daga gare su, sa’an nan za su yi azumi.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi