Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Faburairu 2027 › Faburairu 1

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Faburairu 1, 2027

Litinin · Mako na 4 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Litinin a mako na 4 na lokacin yau da kullum

Ranar mako · Launin ibada: kore

Karatun yini

Karatu na farko

Ibr 11:32–40

32Me kuma zan faɗa? Ba ni da lokacin da zan ba da labari a kan Gideyon, Barak, Samson, Yefta, Dawuda, Sama’ila, da kuma annabawa, 33waɗanda ta wurin bangaskiya ne suka ci nasara a kan mulkoki, suka aikata adalci, suka kuma sami abin da aka yi alkawari; waɗanda suka rurrufe bakunan zakoki, 34suka kashe harshen wuta, suka kuma tsere wa kaifin takobi; waɗanda aka mai da rashin ƙarfinsu ya zama ƙarfi; waɗanda suka yi jaruntaka wajen yaƙi suka kuma fatattaki mayaƙan waɗansu ƙasashe. 35Mata suka karɓi ƙaunatattunsu da aka sāke tasar daga matattu. Aka azabtar da yawancin mutanen nan, amma suka ƙi a sake su, domin sun tabbata za su sami lada mafi kyau sa’ad da aka tā da matattu. 36Waɗansu suka sha ba’a da bulala, har da dauri da sarƙa, da kuma jefa su cikin kurkuku. 37Aka jajjefe su da duwatsu; aka raba su biyu da zarto; aka kashe su da takobi. Suka yi ta yawo saye da fatun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, suka sha tsanani da kuma wulaƙanci 38duniya ba tă ma cancanci su zauna a cikinta ba. Suka yi ta yawo a cikin hamada da a kan duwatsu, da cikin kogwanni da kuma cikin ramummuka. 39Waɗannan duka an yabe su saboda bangaskiyarsu, duk da haka babu waninsu da ya sami abin da aka yi alkawari. 40Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau. Kuma bai so su kai ga maƙasudin bangaskiyarsu ba sai tare da mu.

Zaburar amsawa

Zab 31:19–23

19Alherinka da girma yake, wanda ka ajiye domin waɗanda suke tsoronka, wanda ka mayar a gaban mutane a kan waɗanda suke neman mafaka daga gare ka. 20Cikin inuwar kasancewarka ka ɓoye su daga makircin mutane; a wurin zamanka ka kiyaye su lafiya daga harsuna masu zagi. 21Yabo ya tabbata ga Ubangiji, gama ya nuna ƙaunarsa mai banmamaki gare ni sa’ad da aka yi mini kwanto kewaye da birni. 22Cikin tsorona na ce, “An yanke ni daga gabanka!” Duk da haka ka ji kukata na neman jinƙai sa’ad da na kira gare ka don taimako. 23Ku ƙaunaci Ubangiji, dukanku tsarkakansa! Ubangiji yakan adana amintattu, amma masu girman kai yakan sāka musu cikakke.

Bishara

Mar 5:1–20

1Suka ƙetare tafkin suka je yankin Gerasenawa. 2Da Yesu ya sauka daga jirgin ruwa, sai wani mutum mai mugun ruhu ya fito daga kaburbura, ya tarye shi. 3Wannan mutumin ya mai da kaburbura gidansa. Kuma ba wanda ya iya daure shi, ko da sarƙa ma. 4Gama an sha daure shi hannu da ƙafa da sarƙa, amma yakan tsintsinke sarƙar, yă kuma karye ƙarafan da suke ƙafafunsa. Ba wanda yake da ƙarfin da zai iya yă riƙe shi. 5Dare da rana, sai yă dinga kuka yana ƙuƙƙuje jikinsa da duwatsu a cikin kaburbura da kan tuddai. 6Da ya hangi Yesu daga nesa, sai ya ruga da gudu, ya zo ya durƙusa a gabansa. 7Ya yi ihu da babbar murya ya ce, “Ina ruwanka da ni Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ka rantse da Allah cewa ba za ka ba ni azaba ba!” 8Gama Yesu ya riga ya ce masa, “Ka fita daga jikin mutumin nan, kai mugun ruhu!” 9Sai Yesu ya tambaye shi ya ce, “Mene ne sunanka?” Sai ya amsa ya ce, “Sunana Lejiyon, wato, ‘Tuli,’ domin muna da yawa.” 10Sai ya yi ta roƙon Yesu, kada yă kore su daga wurin. 11A kan tudun da yake nan kusa kuwa, akwai wani babban garken aladu, suna kiwo. 12Sai aljanun suka roƙi Yesu, suka ce, “Tura mu cikin aladun nan, ka bari mu shiga cikinsu.” 13Ya kuwa yarda musu, sai mugayen ruhohin suka fita suka shiga cikin aladun. Garken kuwa, yana da kusan aladu dubu biyu, suka gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, suka nutse. 14Masu kiwon aladun kuwa suka ruga da gudu zuwa cikin gari da ƙauyuka, suka ba da wannan labari. Sai mutanen suka fito, domin su ga abin da ya faru. 15Da suka kai wajen Yesu, sai suka ga mutumin da dā yake da tulin aljanun yana zaune a wurin, sanye da tufafi kuma cikin hankalinsa, sai suka ji tsoro. 16Waɗanda suka ga abin da ya faru, suka ba da labarin abin da ya faru da mai aljanun, da kuma aladun. 17Sai mutane suka fara roƙon Yesu yă bar yankinsu. 18Yesu yana kan shiga cikin jirgin ruwa ke nan, sai mutumin da dā yake da aljanun ya roƙa yă bi shi. 19Yesu bai yardar masa ba, amma ya ce, “Ka tafi gida wurin iyalinka, ka gaya musu babban alherin da Ubangiji ya yi maka, da yadda ya yi maka jinƙai.” 20Sai mutumin ya tafi, ya yi ta ba da labari a cikin Dekafolis a kan babban alherin da Yesu ya yi masa. Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi