Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Janairu 2027 › Janairu 31

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Janairu 31, 2027

Lahadi · Mako na 4 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Lahadi ta 4 ta lokacin yau da kullum

Lahadi · Launin ibada: kore

Karatun yini

Karatu na farko

M Sh 18:15–20

15Ubangiji Allahnku zai tayar muku da wani annabi kamar ni daga cikin ’yan’uwanku. Dole ku saurare shi. 16Gama abin da kuka nema daga Ubangiji Allahnku ke nan a Horeb, a ranar taro, sa’ad da kuka ce, “Kada ka bari mu ji muryar Ubangiji Allahnmu, ko mu ƙara ganin wuta mai girma, in ba haka ba, za mu mutu.” 17Sai Ubangiji ya ce mini, “Abin da suka faɗa yana da kyau. 18Zan tayar musu da wani annabi kamar ka daga cikin ’yan’uwansu; zan sa kalmomina a cikin bakinsa, zai kuma faɗa musu kome da na umarce shi. 19Duk wanda bai saurari kalmomina da annabin nan yake magana da sunana ba, ni kaina zan nemi hakki a kan mutumin. 20Amma duk annabin da ya ɗauka cewa yana magana da sunana a kan wani abin da ban umarce shi ya faɗa ba, ko kuwa wani annabin da ya yi magana da sunan waɗansu alloli, dole a kashe shi.”

Zaburar amsawa

Zab 95:1–2, 6–9

1Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji; bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu. 2Bari mu zo gabansa da godiya mu rera gare shi da kiɗi da waƙa. 6Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada, bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu; 7gama shi ne Allahnmu mu mutanen makiyayansa ne, garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa. Yau, in kuka ji muryarsa, 8“Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba, kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa a hamada, 9inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni, ko da yake sun ga abin da na yi.

Karatu na biyu

1Kor 7:32–35

32Zan so ku ’yantu daga damuwa. Mutum marar aure ya damu ne da al’amuran Ubangiji, yadda zai gamshi Ubangiji. 33Amma mutumin da yake da aure yakan damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda zai gamshi matarsa 34hankalinsa a rabe yake. Mace marar aure ko kuwa budurwa ta damu ne da al’amuran Ubangiji. Nufinta shi ne ta ba da kanta ga Ubangiji cikin jiki da ruhu. Amma mace da take da aure ta damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda za tă gamshi mijinta. 35Na faɗa haka don amfaninku ne, ba don in ƙuntata muku ba. Sai dai don ku yi rayuwa a hanyar da ta dace da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.

Bishara

Mar 1:21–28

21Suka tafi Kafarnahum. Da ranar Asabbaci ta kewayo, sai Yesu ya shiga majami’a ya fara koyarwa. 22Mutane suka yi mamakin koyarwarsa, domin ya koyar da su kamar wanda yake da iko, ba kamar malaman dokoki ba. 23Nan take, sai wani mutum mai mugun ruhu a majami’arsu, ya ɗaga murya ya ce, 24“Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki nan na Allah!” 25Yesu ya tsawata masa ya ce, “Yi shiru! Fita daga cikinsa!” 26Sai mugun ruhun ya jijjiga mutumin da ƙarfi, ya fita daga jikinsa da ihu. 27Dukan mutane suka yi mamaki, suna tambayar juna suna cewa, “Mene ne haka? Tabɗi! Yau ga sabuwar koyarwa kuma da iko! Yana ma ba wa mugayen ruhohi umarni, suna kuma yin masa biyayya.” 28Labari game da shi ya bazu nan da nan ko’ina a dukan yankin Galili.

Tsarkakan ranar

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi