Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Disamba 2026 › Disamba 9
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Disamba 9, 2026
Laraba · Mako na 2 na lokacin Zuwan Ubangiji
Bukukuwa da waliyyai
Laraba a mako na 2 na lokacin Zuwan Ubangiji
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: shunayya
Waliyyi Juan Diego Cuauhtlatoatzin · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
25“Ga wa za ku kwatanta ni? Ko kuwa wa yake daidai da ni?” In ji Mai Tsarkin nan. 26Ku ɗaga idanunku ku duba sammai. Wane ne ya halicce dukan waɗannan? Wane ne ya fitar da rundunar taurari ɗaya-ɗaya, yana kiransu, kowanne da sunansa. Saboda ikonsa mai girma da kuma ƙarfinsa mai girma, babu ko ɗayansu da ya ɓace. 27Ya Yaƙub, ya Isra’ila, me ya sa kake ce kana kuma gunaguni cewa, “Hanyata tana a ɓoye daga Ubangiji; Allah bai kula da abin da yake damuna ba”? 28Ba ku sani ba? Ba ku ji ba? Ubangiji madawwamin Allah ne, Mahaliccin iyakokin duniya. Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba, kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum. 29Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi. 30Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala, samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi; 31amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji za su sabunta ƙarfinsu. Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa; za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba, za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
Zaburar amsawa
1Ta Dawuda. Yabi Ubangiji, ya raina; dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki. 2Yabi Ubangiji, ya raina, kada kuma ka manta dukan alheransa, 3wanda yake gafarta dukan zunubai yake kuma warkar da dukan cututtuka, 4wanda ya fanshi ranka daga rami ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi, 8Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna. 10ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu.
Bishara
28“Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Juan Diego Cuauhtlatoatzin
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi