Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Disamba 2026 › Disamba 10
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Disamba 10, 2026
Alhamis · Mako na 2 na lokacin Zuwan Ubangiji
Bukukuwa da waliyyai
Alhamis a mako na 2 na lokacin Zuwan Ubangiji
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: shunayya
Uwargidanmu ta Loreto · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
13Gama ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya riƙe ka da hannun damana ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro; zan taimake ka. 14Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub marar ƙarfi, ya ƙaramin Isra’ila, gama ni kaina zan taimake ka,” in ji Ubangiji, Mai Fansarka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila. 15“Duba, zan sa ka cikin abin sussuka, saboda kuma mai kaifi mai haƙora da yawa. Za ka yi sussukar duwatsu ka ragargaza su, ka kuma farfashe tuddai su zama kamar yayi. 16Za ka tankaɗe su, iska kuma ta kwashe su, guguwa kuma za tă warwatsa su. Amma za ka yi farin ciki a cikin Ubangiji ka kuma ɗaukaka a cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila. 17“Matalauta da mabukata suna neman ruwa, amma babu kome; harsunansu sun bushe saboda ƙishi. Amma Ni Ubangiji zan amsa musu; Ni, Allah na Isra’ila, ba zan yashe su ba. 18Zan sa koguna su malalo a ƙeƙasassun tuddai, maɓulɓulan ruwa kuma a kwaruruka. Zan mai da hamada tafkunan ruwa, busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓulɓulan ruwa. 19Zan sa a hamada ta tsiro da al’ul da itacen ƙirya, da itacen ci-zaƙi, da zaitun. Zan sa itace mai girma a ƙasashe masu sanyi ya tsiro a ƙeƙasasshiyar ƙasa, tare da fir da kuma saifires, 20don mutane su gani su kuma sani, su lura su kuma fahimci, cewa hannun Ubangiji ne ya aikata haka, cewa Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya sa abin ya faru.
Zaburar amsawa
1Zabura ce ta yabo. Ta Dawuda. Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki; zan yabi sunanka har abada abadin. 9Ubangiji nagari ne ga duka; yana tausayin dukan abubuwan da ya yi. 10Dukan abubuwan da ka yi za su yabe ka, ya Ubangiji; tsarkakanka za su ɗaukaka ka. 11Za su yi maganar ɗaukakar mulkinka za su kuma yi zancen ikonka, 12saboda dukan mutane su san manyan ayyukanka da ɗaukakar darajar mulkinka. 13Mulkinka madawwamin mulki ne, sarautarka kuma za tă dawwama cikin dukan zamanai. Ubangiji mai aminci ne ga dukan alkawuransa mai ƙauna kuma ga dukan abubuwan da ya yi.
Bishara
11Gaskiya nake gaya muku. A cikin dukan waɗanda mata suka haifa, ba wani da ya taso da ya fi Yohanna Mai Baftisma girma; duk da haka mafi ƙanƙanta a mulkin sama ya fi shi girma. 12Tun daga kwanakin Yohanna Mai Baftisma har yă zuwa yanzu, mulkin sama yana sha da ƙyar, fitanannu kuma sun kama mulkin sama sun riƙe gam. 13Gama dukan Annabawa da kuma Doka sun yi ta annabci har yă zuwa kan Yohanna. 14In kuna niyya ku yarda da wannan, to, shi ne Iliya da dā ma zai zo. 15Duk mai kunnen ji, yă ji.
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi