Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2026 › Oktoba 25
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Oktoba 25, 2026
Lahadi · Mako na 30 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Lahadi ta 30 ta lokacin yau da kullum
Lahadi · Launin ibada: kore
Karatun yini
Karatu na farko
21“Kada a wulaƙanta, ko a zalunci baƙo, domin dā ku baƙi ne a ƙasar Masar. 22“Kada ku ci zalin gwauruwa, ko maraya. 23In kuka yi haka, idan kuma suka yi kuka gare ni, zan ji kukansu. 24Zan husata, in kuma kashe ku da takobi; matanku kuma, su ma su zama gwauraye, ’ya’yanku kuwa su zama marayu. 25“In kun ba wa jama’ata matalauta da suke tsakaninku bashin kuɗi, kada ku zama kamar masu ba da rance; kada ku sa yă biya da ruwa. 26In kun ɗauki mayafi maƙwabcinku a matsayin jingina, ku mayar masa kafin fāɗuwar rana, 27domin mayafin ne abin da yake da shi na rufe jikinsa. To, da me zai rufu yă yi barci? Sa’ad da ya yi mini kuka, zan ji, gama ni mai tausayi ne.
Zaburar amsawa
1Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji. Ya rera ta ga Ubangiji kalmomin wannan waƙa sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa da kuma daga hannun Shawulu, ya ce, Ina ƙaunarka, ya Ubangiji, ƙarfina. 2Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona; Allahna shi ne dutsena, a gare shi nake neman mafaka. Shi ne garkuwata da ƙahon cetona, mafakata. 3Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa kuɓuta daga abokan gābana. 46Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga Dutsena! Girma ya tabbata ga Allah Mai cetona! 50Yakan ba sarkinsa nasarori; yakan nuna alheri marar ƙarewa ga shafaffensa, ga Dawuda da zuriyarsa har abada.
Karatu na biyu
5domin bishararmu ba tă zo gare ku da kalmomi kawai ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma cikakken tabbaci. Kun san irin rayuwar da muka yi a cikinku don amfaninku. 6Har kuka zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji; duk da tsananin wahala, kuka karɓi saƙon nan da farin ciki wanda Ruhu Mai Tsarki ya bayar. 7Ta haka kuwa kuka zama gurbi ga dukan masu bi a Makidoniya da Akayya. 8Saƙon Ubangiji ya fito daga gare ku ne ba a Makidoniya da Akayya kaɗai ba bangaskiyarku ga Allah ta zama sananne ko’ina. Saboda haka ba ma bukata mu faɗa wani abu a kai, 9gama su kansu su suke ba da labari irin karɓar da kuka yi mana. Suna faɗin yadda kuka juyo ga Allah daga gumaka don ku bauta wa Allah rayayye da kuma na gaskiya, 10ku kuma jira dawowar Ɗansa daga sama, wanda ya tasa daga matattu, Yesu, wanda ya cece mu daga fushi mai zuwa.
Bishara
34Da jin Yesu ya ƙure Sadukiyawa, sai Farisiyawa suka tattaru. 35Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Doka, ya gwada shi da wannan tambaya. 36“Malam, wace doka ce mafi girma a cikin dokoki?” 37Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’ 38Wannan, ita ce doka ta fari da kuma mafi girma. 39Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ 40Dukan Doka da Annabawa suna rataya ne a kan waɗannan dokoki biyu.”
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi A, shekarar ranakun mako II.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi