Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2026 › Oktoba 2

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Oktoba 2, 2026

Juma’a · Mako na 26 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Juma’a a mako na 26 na lokacin yau da kullum

Tunawa · Launin ibada: fari

Mala’iku masu tsaro tsarkaka · Tunawa

Azumi da tuba

Ranar tuba

Kowace Juma’a ranar tuba ce; kowace taron bishop-bishop yana tsara yadda ake kiyaye ta: kamewa daga nama ko wani aikin tuba. Azumi ya wajaba daga shekara 18 zuwa 59, kamewa daga shekara 14.

Karatun yini

Karatu na farko

Ayu 38:1, 12–21; 40:3–4

1Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba. Ya ce, 12“Ko ka taɓa ba safiya umarni ko kuma ka sa asuba ta fito, 13don ta kama gefen duniya ta kakkaɓe mugaye daga cikinta? 14Ƙasa ta sāke siffa kamar laka da aka yi wa hatimi; ta fito a fili kamar riga. 15An hana mugaye haskensu, hannun da suka ɗaga an karya shi. 16“Ko ka taɓa tafiya zuwa maɓulɓulan teku, ko kuma ka taɓa zuwa cikin zurfin lungun teku? 17Ko an taɓa nuna maka ƙofar mutuwa? Ko ka taɓa ganin ƙofar inuwar duhun mutuwa? 18Ko ka gane fāɗin duniya? Gaya mini, in ka san wannan duka. 19“Ina ne hanyar zuwa gidan haske? Kuma a ina duhu yake zama? 20Ko za ka iya kai su wurarensu? Ka san hanyar zuwa wurin da suke zama? 21Ba shakka ka sani, gama an riga an haife ka a lokacin! Ka yi shekaru da yawa kana rayuwa. 40:3Sai Ayuba ya amsa wa Ubangiji, 4“Ai, ni ba a bakin kome nake ba ne, ta yaya zan iya amsa maka? Na rufe bakina da hannuna.

Zaburar amsawa

Zab 139:1–3, 7–10, 13–14

1Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Ya Ubangiji, ka bincike ni ka kuwa san ni. 2Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi; ka san tunanina daga nesa. 3Ka san fitata da kuma kwanciyata; ka saba da dukan hanyoyina. 7Ina zan tafi daga Ruhunka? Ina zan gudu in tafi daga gabanka? 8In na haura zuwa sammai, kana a can; in na yi gado a zurfafa, kana a can. 9In na tashi a fikafikan safiya, in na sauka a gefe mai nisa na teku, 10can ma hannunka zai bishe ni, hannunka na dama zai riƙe ni gam. 13Gama ka halicci ciki-cikina; ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata. 14Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki; ayyukanka suna da banmamaki, na san da haka sosai.

Bishara

Mat 18:1–5, 10

1A lokacin nan sai almajirai suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Wane ne mafi girma a mulkin sama?” 2Sai ya kira ƙaramin yaro ya sa shi yă tsaya a tsakiyarsu. 3Sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba. 4Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar wannan yaro, shi ne mafi girma a mulkin sama. 5Duk kuma wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan a cikin sunana ya karɓe ni ne. 10“Ku lura, kada ku rena ɗaya daga cikin waɗannan ƙanana. Gama ina faɗa muku mala’ikunsu a sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin sama.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi A, shekarar ranakun mako II.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi