Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2026 › Oktoba 3

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Oktoba 3, 2026

Asabar · Mako na 26 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Asabar a mako na 26 na lokacin yau da kullum

Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore

Tunawa da Budurwa Maryamu Mai Albarka a ranar Asabar · Tunawa da ba dole ba

Karatun yini

Karatu na farko

Ayu 42:1–3, 5–6, 12–17

1Sa’an nan Ayuba ya amsa wa Ubangiji, 2“Na san cewa za ka iya yin dukan abubuwa; ba wanda zai iya ɓata shirinka. 3Ka yi tambaya, ‘Wane ne wannan da ya ƙi karɓar shawarata shi marar ilimi?’ Ba shakka na yi magana game da abubuwan da ban gane ba, abubuwan ban al’ajabi da sun fi ƙarfin ganewata. 5Kunnuwana sun ji game da kai amma yanzu na gan ka. 6Saboda haka na rena kaina na kuma tuba cikin ƙura da toka.” 12Ubangiji ya albarkaci ƙarshen Ayuba fiye da farkonsa. Yana da tumaki guda dubu goma sha huɗu, raƙuma guda dubu shida; shanun noma guda dubu da jakuna guda dubu. 13Ya kuma haifi ’ya’ya maza bakwai, mata uku. 14’Yar farko ya kira ta Yemima, ta biyun Keziya ta ukun Keren-Haffuk. 15Duk a cikin ƙasar ba a samu kyawawan mata kamar ’ya’yan Ayuba ba, kuma babansu ya ba su gādo tare ta ’yan’uwansu maza. 16Bayan wannan Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba’in; ya ga ’ya’yansa da ’ya’yansu har tsara ta huɗu. 17Sa’an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa.

Zaburar amsawa

Zab 119:66, 71, 75, 91, 125, 130

66Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau, gama na gaskata a umarnanka. 71Ya yi kyau da na sha wahala don in koyi ƙa’idodinka. 75Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne, kuma cikin aminci ka hore ni. 91Dokokinka sun dawwama har yă zuwa yau, gama dukan abubuwa suna maka hidima. 125Ni bawanka ne, ka ba ni fahimi don in gane farillanka. 130Fassarar maganganunka sukan ba da haske; sukan ba da ganewa ga marar ilimi.

Bishara

Luk 10:17–24

17Mutum saba’in da biyun nan suka dawo da murna, suka ce, “Ubangiji, har mun sha ƙarfin aljanu ma a cikin sunanka.” 18Sai ya amsa ya ce, “Na ga Shaiɗan ya fāɗi daga sama kamar walƙiya. 19Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku. 20Duk da haka, kada ku yi farin ciki da cewa, kun sha ƙarfin ruhohi, amma ku yi farin ciki, domin an rubuta sunayenku a sama.” 21A wannan lokaci, Yesu, cike da murna ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Na yabe ka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima, da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. I, ya Uba, gama wannan shi ne nufinka mai kyau. 22“Ubana ya danƙa mini dukan kome. Ba wanda ya san Ɗan sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban, sai Ɗan, da kuma waɗanda Ɗan ya zaɓa ya bayyana musu shi.” 23Sai ya juya wajen almajiransa, ya ce musu a ɓoye, “Albarka ga idanun da suka ga abin da kuke gani. 24Ina faɗa muku, annabawa da sarakuna da yawa sun so su ga abin nan da kuke gani, amma ba su gani ba. Sun so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.”

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi A, shekarar ranakun mako II.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi