Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2026 › Oktoba 1
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Oktoba 1, 2026
Alhamis · Mako na 26 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Alhamis a mako na 26 na lokacin yau da kullum
Tunawa · Launin ibada: fari
Waliyya Thérèse ta Yesu Jariri, budurwa kuma malamar Ikkilisiya · Tunawa
Karatun yini
Karatu na farko
21“Ku tausaya mini, abokaina, ku ji tausayina, gama hannun Allah ya sauko a kaina. 22Don me kuke fafarata kamar yadda Allah yake yi? Ba ku gaji da yagar fatata ba? 23“Kash, da ma a ce ana rubuta maganganuna, da an rubuta su a littafi, 24a rubuta su da ƙarfe a kan dutse don su dawwama har abada! 25Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai, kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya. 26Kuma bayan an hallaka fatata, duk da haka a cikin jiki zan ga Allah. 27Zan gan shi da kaina da idanuna, Ni, ba wani ba ne. Zuciyata ta cika da wannan tunani!
Zaburar amsawa
7Ka ji muryata sa’ad da na yi kira, ya Ubangiji; ka yi mini jinƙai ka kuma amsa mini. 8Zuciyata kan faɗa game da kai, “Nemi fuskarsa!” Fuskarka, Ubangiji, zan nema. 9Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni, kada ka kore bawanka daga gare ka cikin fushi; kai ne ka kasance mai taimakona. Kada ka ƙi ni ko ka yashe ni, Ya Allah Mai cetona. 13Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewa zan ga alherin Ubangiji; a ƙasar masu rai. 14Ka dogara ga Ubangiji, ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya ka kuma dogara ga Ubangiji.
Bishara
1Bayan haka, Ubangiji ya naɗa waɗansu mutum saba’in da biyu, ya aike su biyu-biyu, su riga shi yin gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da zai shiga. 2Ya ce musu, “Girbi na da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Saboda haka, ku roƙi Ubangijin girbi ya aikar da ma’aikata zuwa gonarsa. 3Ku tafi! Ina aikan ku kamar tumaki cikin kyarketai. 4Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma. Kada ma ku gai da kowa a kan hanya. 5“Sa’ad da kuka shiga wani gida, ku fara da cewa, ‘Salama a gare ku mutanen gida.’ 6In akwai mutum mai salama a gidan, salamarku za tă kasance tare da shi, in kuwa babu, salamarku za tă koma muku. 7Ku zauna a wannan gidan, kuna ci kuna shan duk abin da suka ba ku, gama ma’aikaci ya cancanci albashinsa. Kada ku yi yawan sāke masauƙi, daga gida zuwa gida. 8“Sa’ad da kuka shiga garin, kuma aka karɓe ku, ku ci ko mene ne da aka ajiye a gabanku. 9Ku warkar da marasa lafiya da suke wurin. Ku kuma faɗa musu cewa, ‘Mulkin Allah yana kusa da ku.’ 10Amma sa’ad da kuka shiga garin, kuma ba a karɓe ku ba, ku bi titi-titi ku ce, 11‘Ko ƙurar garinku da kuke manne a ƙafafunmu, mun karkaɗe muku. Duk da haka, ku tabbatar da wannan, “Mulkin Allah yana kusa.” ’ 12Ina dai faɗa muku, a ranan nan, za a fi jin tausayin Sodom fiye da wannan garin.
Tsarkakan ranar
- Waliyya Thérèse ta Yesu Jariri, budurwa kuma malamar Ikkilisiya
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi A, shekarar ranakun mako II.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi