Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Solomon
Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Solomon
Mutuwar Solomon
1Sar 11:41–43 · 2Tar 9:29–31
1Sar 11:41–4341Game da sauran ayyukan mulkin Solomon, da dukan abubuwan da ya yi, da hikimar da ya nuna, an rubuta su a littafin tarihin Solomon.
42Solomon ya yi mulki a Urushalima, a bisa dukan Isra’ila, shekaru arba’in.
43Sa’an nan ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a birnin Dawuda mahaifinsa. Sai Rehobowam ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
2Tar 9:29–3129Game da sauran ayyukan mulkin Solomon, daga farko har zuwa ƙarshe, an rubuta su a cikin tarihin annabi Natan, cikin annabcin Ahiya mutumin Shilo da kuma cikin wahayin Iddo mai gani game da Yerobowam ɗan Nebat.
30Solomon ya yi mulki a Urushalima a bisa dukan Isra’ila shekaru arba’in.
31Sa’an nan ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi cikin birnin Dawuda mahaifinsa. Rehobowam ɗansa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.
An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY