18:13A shekara ta goma sha huɗu ta mulkin sarkin Hezekiya, sai sarki Sennakerib sarkin Assuriya ya kai farmaki wa biranen Yahuda masu katanga ya kuma kama su.
18:14Sai Hezekiya sarkin Yahuda ya aika saƙo ga sarkin Assuriya a Lakish cewa, “Na yi laifi, ka janye daga gare ni, zan kuma biya ka duk abin da ake bukata daga gare ni.” Sarkin Assuriya ya karɓi talenti ɗari uku na azurfa, da talenti talatin na zinariya daga hannun Hezekiya sarkin Yahuda.
18:15Ya zama kuwa cewa, Hezekiya ya bayar da dukan azurfan da suke a haikalin Ubangiji da kuma a ma’ajin fadan sarki.
18:16A wannan lokaci ne Hezekiya sarkin Yahuda ya ɓaɓɓalle zinariyan da aka dalaye ƙofofi da madogaran ƙofofin haikalin Ubangiji, ya ba sarkin Assuriya.
18:17Sai sarkin Assuriya ya aika da babban shugaban sojojinsa, da shugaban dattawansa, da wakilinsa daga birnin Lakish tare da ƙungiyar sojoji masu yawa zuwa Urushalima domin su yaƙi Sarki Hezekiya. Da suka haura sai suka tsaya a wurin lambatun da yake kawo ruwa daga Tafkin Tudu, kusa da hanyar Filin Mai Wanki.
18:18Suka kira sarki, sai Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka je wurinsu.
18:19Jagoran dogarawan sarkin Assuriya ya ce musu, “Ku ce wa Hezekiya, “ ‘Ga abin da babban sarkin Assuriya ya ce, da wa kake taƙama?
18:20Ka ce kana da dabara da ƙarfin soji, amma bagu kawai kake yi. Da wa ka dogara har da za ka yi mini tawaye?
18:21Na sani kana dogara da Masar, wadda take kamar karar masara, wadda in ka jingina a kai, za tă karye tă soki hannunka. Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga dukan wanda ya dogara da shi.
18:22Sai ya ci gaba da cewa, in kuma ka ce mini “Muna dogara ga Ubangiji Allahnmu ne,” ba masujadansa da bagadansa ne Hezekiya ya ciccire, yana ce wa Urushalima da Yahuda, “Dole ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima”?
18:23“ ‘Yanzu, ka zo ku shirya da shugabana, sarkin Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu, in za ka sami mahayansu!
18:24Yaya za ka yi tsayayya da mafi ƙanƙantan hafsan shugabana, ko da kana dogara da Masar don kekunan yaƙi da mahaya dawakai?
18:25Ban da haka ma, kana gani cewa na zo in hallaka wannan wuri ne ba tare da na ji daga Ubangiji ba? Ubangiji da kansa ne ya ce da ni in kawo wa wannan ƙasa hari in hallaka ta.’ ”
18:26Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa suka ce wa jagoran dakarun, “Muna roƙonka ka yi wa bayinka magana da harshen Arameyik da yake muna ji. Kada ka yi mana magana da Yahudanci domin kada mutanen da suke bisa katanga su ji!”
18:27Amma shugaban sojojin ya ce, “Ai, ba gare ku da sarkinku kaɗai ne shugabana ya aike ni ba. Amma har ga mutanen da suke zaune a kan katangar birnin, waɗanda za su ci kashinsu, su sha fitsarinsu!”
18:28Sai shugaban sojojin ya yi kira da Yahudanci ya ce, “Ku ji muryar babban sarki, sarkin Assuriya!
18:29Ga abin da sarki ya faɗa; kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku. Ba zai iya cetonku daga hannuna ba.
18:30Kada ku yarda Hezekiya yă rinjaye ku cewa ku dogara ga Allah, sa’ad da ya ce da ku, ‘Ba shakka Ubangiji zai cece mu; yana ce da ku birnin nan ba zai faɗa a hannun sarkin Assuriya ba.’
18:31“Kada ku saurari Hezekiya. Ga abin da sarkin Assuriya ya ce, ku shirya zaman lafiya da ni, ku fito zuwa wurina. Kowane ɗayanku kuwa zai ci ’ya’yan inabinsa da ’ya’yan ɓaurensa, yă kuma sha ruwa daga randarsa,
18:32har lokacin da zan zo in kwashe ku, in kai ku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasa mai yalwar hatsi, da ruwan inabi, da abinci, da gonakin inabi, da itatuwan zaitun, da zuma, don ku rayu, kada ku mutu! “Kada ku saurari Hezekiya, don karya yake muku, sa’ad da ya ce, ‘Ubangiji zai cece mu.’
18:33Akwai allahn wata al’ummar da ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannun sarkin Assuriya?
18:34Ina allolin Hamat da na Arfad? Ina allolin Sefarfayim, da na Hena, da na Iffa? Sun cece Samariya daga hannuna?
18:35Wanne a cikin dukan allolin ƙasashen nan ya iya ceton ƙasarsa da gare ni? Shugaban sojojin ya kuma ci gaba da cewa, ta yaya Ubangiji zai ceci Urushalima daga hannuna?”
18:36Amma mutane suka yi shiru ba su amsa masa ba, domin sarki ya umarta cewa, “Kada ku amsa masa.”
18:37Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf, marubuci, suka je wurin Hezekiya da tufafinsu a kece, suka faɗa masa abin da shugaban sojojin ya faɗa.
19:1Da sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya shiga haikalin Ubangiji.
19:2Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna marubuci da shugabannin firistoci, dukansu sanye da tufafin makoki, zuwa wurin annabi Ishaya ɗan Amoz.
19:3Suka ce masa, “Hezekiya ya ce, yau ranar wahala ce, da ta cin mutunci, da ta shan kunya, ga shi, ’ya’ya suna gab da a haife su, amma ba ƙarfin da za a yi yunƙuri a haife su.
19:4Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka ya ji dukan maganganun sarkin yaƙi, wanda maigidansa, sarkin Assuriya, ya aiko don yă rena Allah mai rai. Bari Ubangiji Allahnka yă tsawata masa saboda maganar da ya ji. Saboda haka ka yi addu’a domin raguwar da har yanzu suke a raye.”
19:5Da fadawan sarki Hezekiya suka isa wurin Ishaya,
19:6Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku, in ji Ubangiji, ‘Kada abin da ka ji yă firgita ka, wato, waɗannan kalmomin da karen nan na sarkin Assuriya ya yi saɓo da su.
19:7Saurara! Zan sa masa wani ruhun da zai sa yă ji wata jita-jitar da za tă sa yă koma ƙasarsa. A can zan sa a kashe shi da takobi a ƙasarsa.’ ”
19:8Da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye, ya kuma iske sarkin yana yaƙi da Libna.
19:9To, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush sarkin Masar, yana zuwa masa da yaƙi. Saboda haka ya sāke aika manzanni zuwa wurin Hezekiya cewa,
19:10“Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda, kada ka bar allahn da kake dogara gare shi yă ruɗe ka cewa, ‘Urushalima ba za tă fāɗi a hannun sarkin Assuriya ba.’
19:11Ba shakka ka riga ka ji abin da sarkin Assuriya ya yi da dukan ƙasashe, yana hallaka su gaba ɗaya. Kai kuwa kana ji za a cece ka?
19:12Allolin al’umman da kakannina suka hallaka, sun cece su ne, allolin Gozan, da na Haran, da na Rezef, da kuma na mutane Eden da suke a Tel Assar?
19:13Ina sarkin Hamat, da sarkin Arfad, da sarkin birnin Sefarfayim, ko na Hena da kuma na Iffa?”
19:14Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga manzannin ya karanta. Sa’an nan ya tashi ya tafi haikalin Ubangiji ya shimfiɗa wasiƙar a gaban Ubangiji.
19:15Hezekiya kuwa ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda yake zaune tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah bisa dukan mulkokin duniya. Kai ka yi sama da duniya.
19:16Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka ji; ka buɗe idanunka ya Ubangiji ka gani; ka saurari kalmomin da Sennakerib ya aiko don yă yi wa Allah mai rai ba’a.
19:17“Da gaske ne, ya Ubangiji, cewa sarakunan Assuriya sun hallakar da waɗannan al’ummai da ƙasashensu.
19:18Sun jefar da allolinsu cikin wuta, suka hallaka su, gama ba alloli ba ne, katakai ne da kuma duwatsu, ayyukan hannuwan mutane.
19:19To, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga hannunsa, don dukan mulkokin duniya su san cewa kai kaɗai, ya Ubangiji ne Allah.”
19:20Sai Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo zuwa wurin Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, na ji addu’arka game da Sennakerib sarkin Assuriya.
19:21Ga abin da Ubangiji yana cewa game da shi, “ ‘Budurwar Sihiyona ta rena ka tana kuma yin maka ba’a. Diyar Urushalima ta kaɗa kanta yayinda kake gudu.
19:22Wane ne ka zaga, ka kuma yi masa saɓo? Wa kake gāba da shi har ka ɗaga muryarka, har ka tā da idanunka da fahariya? Kana gāba da Mai Tsarki na Isra’ila!
19:23Ta wurin manzanninka ka tara wa Ubangiji zagi. Ka kuma ce, “Da yawa kekunan yaƙina na haye kan ƙwanƙolin duwatsu, wurin mafi tsawo na Lebanon. Na sassare itacen al’ul nasa mafi tsawo mafi daraja na itacen fir nasa. Na ratsa har can tsakiyar kurmi, mafi kyau na kurminsa.
19:24Na tona rijiyoyi a ƙasashen waje na kuma sha ruwa a can. Da tafin ƙafafuna na busar da dukan rafuffukan Masar.”
19:25“ ‘Ba ka taɓa ji ba? Tun da daɗewa na ƙaddara haka. Tuntuni kuwa na shirya shi; yanzu kuma na sa ya faru, cewa ka mai da birane masu katanga tarin duwatsu.
19:26Ƙarfin mutanensu ya tsiyaye, suka razana aka kuma kunyata su. Suna kama da tsirai a gona, kamar sabon toho kamar ciyawa mai tohuwa bisa rufin ɗaki wanda ya bushe saboda zafi, kafin yă yi girma.
19:27“ ‘Amma na san wurin zamanka da fitarka da shigarka da yadda kake fushi da ni.
19:28Domin kana fushi da ni reninka ya iso kunnuwata, zan sa ƙugiyata a hancinka da linzamina a bakinka, zan kuma sa ka koma a ta hanyar da ka zo.’
19:29“Wannan zai zama alama a gare ka, ya Hezekiya, “Bana, za ku ci amfanin gonar da ya tsira da kansa, baɗi kuma amfanin gonar da ya tsiro daga na bara. Amma a shekara ta uku, za ku yi shuki, ku kuma girbe, ku dasa gonakin inabi, ku kuma ci ’ya’yansa.
19:30Sau ɗaya kuma ragowar masarautar Yahuda za tă yi saiwoyi a ƙasa ta kuma ba da ’ya’ya a bisa.
19:31Gama daga Urushalima za a sami ragowa, daga Dutsen Sihiyona kuma za a sami waɗanda suka tsira. Himmar Ubangiji Maɗaukaki za tă cika wannan.
19:32“Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce game da sarkin Assuriya, “Ba zai shiga birnin nan ba ko yă harba kibiya a nan. Ba zai kusace ta da garkuwa ko yă yi mata zoben yaƙi ba.
19:33Ta hanyar da ya zo ne zai koma; ba zai shiga birnin nan ba, in ji Ubangiji.
19:34Zan kāre birnin nan in cece ta, saboda kaina da kuma bawana Dawuda.”
19:35A daren nan mala’ikan Ubangiji ya fita ya kashe dakaru dubu ɗari da tamanin da biyu a sansanin Assuriyawa. Da mutane suka farka da safe, sai ga gawawwaki ko’ina.
19:36Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya tā da sansanin ya kuma janye. Ya koma Ninebe ya zauna a can.
19:37Wata rana yayinda yake sujada a haikalin Nisrok, allahnsa, sai ’ya’yansa maza, Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka gudu zuwa ƙasar Ararat. Sai Esar-Haddon ɗansa ya gāje shi.