17A wannan lokaci, Hazayel sarkin Aram ya haura, ya kai wa Gat hari, ya kuma ci ta da yaƙi. Sa’an nan ya juya don yă yaƙi Urushalima.
18Amma Yowash sarkin Yahuda ya kwashe tsarkakan kayan da kakanninsa, Yehoshafat, Yehoram da Ahaziya, sarakunan Yahuda suka keɓe, da kyautai da shi kansa ya keɓe, da kuma dukan azurfan da aka samu a ɗakunan ajiya haikalin Ubangiji da na fada, ya aika da su wa Hazayel sarkin Aram, shi kuma ya janye daga Urushalima.
19Game da sauran ayyukan mulkin Yowash da duk abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.
20Hafsoshinsa suka yi masa maƙarƙashiya suka kashe shi a Bet Millo, a kan hanyar da ta gangara zuwa Silla.
21Hafsoshin da suka kashe shi kuwa su ne Yozabad ɗan Shimeyat da Yehozabad ɗan Shomer. Ya mutu, aka kuma binne shi tare da kakanninsa a Birnin Dawuda. Sai Amaziya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.