Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Urushalima
Littattafan Bishara gefe da gefe · A Urushalima
Yesu ya faɗi game da rushewar haikali
Mat 24:1–2 · Mar 13:1–2 · Luk 21:5–6
Mat 24:1–21Yesu ya bar haikali ke nan, yana cikin tafiya sai almajiransa suka zo wurinsa don su ja hankalinsa ga gine-ginen haikali.
2Sai Yesu ya ce, “Kun ga duk waɗannan abubuwa? Gaskiya nake gaya muku, ba wani dutse a nan da za a bari a kan wani; duk za a rushe.”
Mar 13:1–21Da yake barin haikalin, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Malam! Dubi irin manya-manyan duwatsun nan! Ka ga irin gine-ginen nan masu kyau mana!”
2Yesu ya amsa ya ce, “Ka ga dukan manyan gine-ginen nan? Ba wani dutse a nan, da za a bari kan wani da ba za a rushe ba.”
Luk 21:5–65Waɗansu daga cikin almajiransa, suka fara magana a kan yadda aka yi wa haikalin ado da duwatsu masu kyau, da kuma kyautai da aka keɓe wa Allah. Amma Yesu ya ce,
6“Wannan abin da kuke kallo a nan, lokaci yana zuwa da ba za a bar wani dutse a kan wani dutse ba. Kowannensu, za a rushe shi.”
An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY