Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Nuwamba 2027 › Nuwamba 8

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Nuwamba 8, 2027

Litinin · Mako na 32 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Litinin a mako na 32 na lokacin yau da kullum

Ranar mako · Launin ibada: kore

Karatun yini

Karatu na farko

Ba ya cikin wannan fassara

Zaburar amsawa

Zab 139:1–10

1Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Ya Ubangiji, ka bincike ni ka kuwa san ni. 2Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi; ka san tunanina daga nesa. 3Ka san fitata da kuma kwanciyata; ka saba da dukan hanyoyina. 4Kafin in yi magana da harshena ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji. 5Ka kewaye ni, gaba da baya; ka sa hannunka a kaina. 6Irin wannan sanin game da ni ya fi ƙarfin magana, ya fi ƙarfi in gane. 7Ina zan tafi daga Ruhunka? Ina zan gudu in tafi daga gabanka? 8In na haura zuwa sammai, kana a can; in na yi gado a zurfafa, kana a can. 9In na tashi a fikafikan safiya, in na sauka a gefe mai nisa na teku, 10can ma hannunka zai bishe ni, hannunka na dama zai riƙe ni gam.

Bishara

Luk 17:1–6

1Yesu ya ce wa almajiransa, “Dole ne a sami abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi, amma kaiton mutumin nan wanda suke zuwa ta wurinsa. 2Gwamma a ɗaura dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku, da ya sa ɗaya daga cikin ƙananan yaran nan ya yi zunubi. 3Saboda haka, ku lura da kanku. “In ɗan’uwanka ya yi zunubi, ka kwaɓe shi. In ya tuba, ka gafarta masa. 4In ya yi maka laifi sau bakwai a rana ɗaya, ya kuma dawo sau bakwai ɗin a wurinka, yana cewa, ‘Na tuba,’ sai ka gafarta masa.” 5Sai manzannin suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya!” 6Ya amsa musu ya ce, “In kuna da bangaskiya da take ƙanƙani kamar ƙwayar mustad, kuna iya ce wa wannan itacen durumi, ‘Ka tumɓuke daga nan, ka dasu a cikin teku.’ Zai kuwa yi muku biyayya.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi