Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2027 › Oktoba 29

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Oktoba 29, 2027

Juma’a · Mako na 30 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Juma’a a mako na 30 na lokacin yau da kullum

Ranar mako · Launin ibada: kore

Azumi da tuba

Ranar tuba

Kowace Juma’a ranar tuba ce; kowace taron bishop-bishop yana tsara yadda ake kiyaye ta: kamewa daga nama ko wani aikin tuba. Azumi ya wajaba daga shekara 18 zuwa 59, kamewa daga shekara 14.

Karatun yini

Karatu na farko

Rom 9:1–5

1Ina faɗin gaskiya a cikin Kiristi ba ƙarya nake yi ba, lamirina ya tabbatar da wannan a cikin Ruhu Mai Tsarki. 2Ina da baƙin ciki mai yawa da kuma rashin kwanciyar rai marar ƙarewa a zuciyata. 3Gama da so na ne, sai a la’anta ni a kuma raba ni da Kiristi saboda ’yan’uwana, waɗannan na kabilata, 4mutanen Isra’ila. Su ne Allah ya mai da su ’ya’yansa, ya bayyana musu ɗaukakarsa, ya ba su alkawarinsa da Dokarsa, ya nuna musu hanyar sujada ta gaske, ya kuma ba su sauran alkawura. 5Kakannin-kakannin nan kuma nasu ne, Kiristi kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo ya tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome! Amin.

Zaburar amsawa

Zab 147:12–15, 19–20

12Ki ɗaukaka Ubangiji, ya Urushalima; ki yabi Allahnki, ya Sihiyona. 13Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinki yana kuma albarkace mutanenki a cikinki. 14Yana ba da salama ga iyakokinki yana kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau. 15Yana ba da umarninsa ga duniya; maganarsa tana tafiya da sauri. 19Ya bayyana maganarsa ga Yaƙub, dokokinsa da ƙa’idodinsa ga Isra’ila. 20Bai yi wannan ga wata al’umma ba; ba su san dokokinsa ba. Yabi Ubangiji.

Bishara

Luk 14:1–6

1Wata ranar Asabbaci, da Yesu ya shiga gidan wani sanannen Bafarisiye don cin abinci, sai mutane suka zuba masa ido da kyau. 2A nan a gabansa kuwa akwai wani mutum mai ciwon kumburin ƙafa da hannu. 3Sai Yesu ya tambayi masanan dokoki da Farisiyawa ya ce, “Daidai ne bisa ga doka, a yi warkarwa a ranar Asabbaci, ko babu?” 4Amma ba su ce kome ba. Sai ya riƙe mutumin, ya warkar da shi, sa’an nan ya sallame shi. 5Sai ya tambaye, su ya ce, “In wani a cikinku yana da ɗa, ko bijimi da ya faɗa a rijiya a ranar Asabbaci, ba za ku cire shi nan da nan ba?” 6Suka rasa abin faɗi.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi