Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2027 › Oktoba 22
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Oktoba 22, 2027
Juma’a · Mako na 29 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Juma’a a mako na 29 na lokacin yau da kullum
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore
Waliyyi John Paul na II, Fafaroma · Tunawa da ba dole ba
Azumi da tuba
Ranar tuba
Kowace Juma’a ranar tuba ce; kowace taron bishop-bishop yana tsara yadda ake kiyaye ta: kamewa daga nama ko wani aikin tuba. Azumi ya wajaba daga shekara 18 zuwa 59, kamewa daga shekara 14.
Karatun yini
Karatu na farko
18Gama na san cewa babu wani abin kirkin da yake zaune a cikina, wato, a mutuntakata. Gama sha’awar yin abu mai kyau kam ina da ita, sai dai ikon yin ne fa babu. 19Gama abin da nake yi ba shi ne abu mai kyau da nake so in yi ba; a’a, mugun da ba na so in yi, shi ne nake ci gaba da yi. 20To, in na yi abin da ba na so in yi, ba ni ba ne nake yinsa, sai dai zunubin nan da yake zaune a cikina. 21Saboda haka na gane wannan ƙa’ida ce take aiki a cikina. Sa’ad da nake so in yi abu mai kyau, sai in ga cewa mugun nan ne nake yi. 22Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah; 23amma ina ganin wata doka tana aiki a gaɓoɓin jikina, tana yaƙi da dokar hankalina, tana kuma sa in zama ɗaurarren dokar zunubin da take aiki a gaɓoɓin jikina. 24Kaitona! Wane ne zai cece ni daga wannan jiki mai mutuwa? 25Godiya ga Allah ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu! Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.
Zaburar amsawa
66Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau, gama na gaskata a umarnanka. 68Kai nagari ne, kuma abin da kake yi yana da kyau; ka koya mini ƙa’idodinka. 76Bari ƙaunarka marar ƙarewa tă yi mini ta’aziyya, bisa ga alkawarinka ga bawanka. 77Bari tausayinka yă zo mini don in rayu, gama dokarka ce farin cikina. 93Ba zan taɓa manta da farillanka ba, gama ta wurinsu ne ka kiyaye raina. 94Ka cece ni, gama ni naka ne; na yi ƙoƙarin neman farillanka.
Bishara
54Ya ce wa taron, “Sa’ad da kuka ga hadari ya fito daga yamma, nan da nan kukan ce, ‘Za a yi ruwan sama,’ sai a kuwa yi. 55Sa’ad da kuma iska ta taso daga kudu, kukan ce, ‘Za a yi zafi,’ sai kuwa a yi. 56Munafukai! Kuna san yadda za ku fassara yanayin ƙasa da na sararin sama. Ta yaya ba ku san yadda za ku yi fassarar wannan zamani ba? 57“Don me ba ku iya auna wa kanku, abin da yake daidai ba? 58Yayinda kake kan hanyar zuwa kotu da maƙiyinka, ka yi matuƙar ƙoƙari ku shirya tun kuna kan hanya. In ba haka ba, zai kai ka gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga ɗan sanda, ɗan sanda kuma ya jefa ka a kurkuku. 59Ina gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.”
Tsarkakan ranar
- Waliyyi John Paul na II, Fafaroma
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi