Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2027 › Oktoba 2

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Oktoba 2, 2027

Asabar · Mako na 26 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Asabar a mako na 26 na lokacin yau da kullum

Tunawa · Launin ibada: fari

Mala’iku masu tsaro tsarkaka · Tunawa

Karatun yini

Karatu na farko

Ba ya cikin wannan fassara

Zaburar amsawa

Zab 69:32–36

32Matalauta za su gani su kuma yi murna, ku da kuke neman Allah, bari zukatanku su rayu! 33Ubangiji yakan ji masu bukata ba ya kuwa ƙyale kamammun mutanensa. 34Bari sama da ƙasa su yabe shi, tekuna da dukan abin da yake motsi a cikinsu, 35gama Allah zai cece Sihiyona yă sāke gina biranen Yahuda. Sa’an nan mutane za su zauna a can su mallake ta, 36’ya’yan bayinsa za su gāje ta, waɗanda kuma suna ƙaunar sunansa za su zauna a can.

Bishara

Mat 18:1–5, 10

1A lokacin nan sai almajirai suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Wane ne mafi girma a mulkin sama?” 2Sai ya kira ƙaramin yaro ya sa shi yă tsaya a tsakiyarsu. 3Sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba. 4Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar wannan yaro, shi ne mafi girma a mulkin sama. 5Duk kuma wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan a cikin sunana ya karɓe ni ne. 10“Ku lura, kada ku rena ɗaya daga cikin waɗannan ƙanana. Gama ina faɗa muku mala’ikunsu a sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin sama.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi