Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2027 › Oktoba 1
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Oktoba 1, 2027
Juma’a · Mako na 26 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Juma’a a mako na 26 na lokacin yau da kullum
Tunawa · Launin ibada: fari
Waliyya Thérèse ta Yesu Jariri, budurwa kuma malamar Ikkilisiya · Tunawa
Azumi da tuba
Ranar tuba
Kowace Juma’a ranar tuba ce; kowace taron bishop-bishop yana tsara yadda ake kiyaye ta: kamewa daga nama ko wani aikin tuba. Azumi ya wajaba daga shekara 18 zuwa 59, kamewa daga shekara 14.
Karatun yini
Karatu na farko
Ba ya cikin wannan fassara
Zaburar amsawa
1Zabura ta Asaf. Ya Allah, al’ummai sun mamaye gādonka; sun ƙazantar da haikalinka mai tsarki, sun bar Urushalima kufai. 2Sun ba da gawawwakin bayinka kamar abinci ga tsuntsayen sararin sama, nama jikin tsarkakanka ga namun jejin duniya. 3Sun zubar da jini kamar ruwa ko’ina a Urushalima, kuma babu wani da zai binne matattu. 4Mun zama abin reni ga maƙwabta, abin ba’a da reni ga waɗanda suke kewaye da mu. 5Har yaushe, ya Ubangiji za ka yi ta fushi? Har abada ne? Har yaushe kishinka zai yi ta ƙuna kamar wuta? 8Kada ka riƙe zunubai kakanni a kanmu; bari jinƙanka yă zo da sauri yă sadu da mu, gama mun fid da zuciya sarai. 9Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu, saboda ɗaukakar sunanka; ka cece mu ka kuma gafarta mana zunubanmu saboda sunanka.
Bishara
13“ ‘Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida!’ Ai, da a ce a Taya da Sidon ne aka yi ayyukan banmamaki da aka yi a cikinku, da tuni sun tuba, suna zama cikin rigar makoki da toka. 14A ranar shari’a, za a fi jin tausayin Taya da Sidon fiye da ku. 15Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani za ki sami ɗaukaka ne? A’a, za a hallaka ki. 16“Wanda ya saurare ku, ni yake saurara. Wanda ya ƙi ku, ni yake ƙi. Amma wanda ya ƙi ni kuwa, ya ƙi wanda ya aiko ni ne.”
Tsarkakan ranar
- Waliyya Thérèse ta Yesu Jariri, budurwa kuma malamar Ikkilisiya
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi