Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Satumba 2027 › Satumba 27

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Satumba 27, 2027

Litinin · Mako na 26 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Litinin a mako na 26 na lokacin yau da kullum

Tunawa · Launin ibada: fari

Waliyyi Vincent de Paul, firist · Tunawa

Karatun yini

Karatu na farko

Zak 8:1–8

1Maganar Ubangiji Maɗaukaki ta sāke zuwa gare ni. 2Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ina kishin Sihiyona ƙwarai; ina kuma cike da kishi dominta.” 3Ga abin da Ubangiji ya ce, “Zan koma Sihiyona in zauna a Urushalima. Sa’an nan za a kira Urushalima Birnin Gaskiya, a kuma kira dutsen Ubangiji Maɗaukaki Dutse Mai Tsarki.” 4Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Tsofaffi maza da mata za su sāke zauna a titunan Urushalima, kowanne da sanda a hannu saboda tsufa. 5Titunan birnin za su cika da samari da ’yan mata suna wasa.” 6Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Mai yiwuwa ya zama da mamaki ga raguwar wannan mutanen da suke nan a lokacin, amma zai zama abin mamaki gare ni ne?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. 7Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Zan ceci mutanena daga ƙasashen gabas da yamma. 8Zan komo da su su zauna a Urushalima; za su zama mutanena, ni kuwa zan zama amintaccen Allahnsu mai adalci.”

Zaburar amsawa

Zab 102:15–20, 28, 21–22

15Al’ummai za su ji tsoron sunan Ubangiji, dukan sarakunan duniya za su girmama ɗaukakarka. 16Gama Ubangiji zai sāke gina Sihiyona ya kuma bayyana a ɗaukakarsa. 17Zai amsa addu’ar marasa ƙarfi; ba zai ƙyale roƙonsu ba. 18Bari a rubuta wannan don tsara mai zuwa, cewa mutanen da ba a riga an halitta ba za su yabi Ubangiji, 19“ Ubangiji ya duba ƙasa daga wurinsa mai tsarki a bisa, daga sama ya hangi duniya, 20don yă ji nishe-nishen ’yan kurkuku yă kuma saki waɗanda aka yanke musu hukuncin mutuwa.” 28’Ya’yan bayinka za su zauna a gabanka; zuriyarsu za su kahu a gabanka.” 21Saboda haka za a furta sunan Ubangiji a Sihiyona yabonsa kuma a Urushalima 22sa’ad da mutane da mulkoki suka tattaru don su yi wa Ubangiji sujada.

Bishara

Luk 9:46–50

46Wata gardama ta tashi a tsakanin almajiran, a kan ko wane ne a cikinsu zai zama mafi girma 47Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa ya tsaya kusa da shi. 48Sai ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi wannan ƙaramin yaron a cikin sunana, ni ya karɓa, kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne. Gama mafi ƙanƙanta duka a cikinku, shi ne kuma mafi girma.” 49Sai Yohanna ya ce, “Ubangiji, mun ga wani mutum yana fitar da aljanu a cikin sunanka, muka yi ƙoƙarin hana shi, don shi ba ɗaya ba ne daga cikinmu.” 50Yesu ya ce, “Kada ku hana shi, gama duk wanda ba ya gāba da ku, naku ne.”

Tsarkakan ranar

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi