Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Satumba 2027 › Satumba 14

Kalandar Ortodoks · 1 ga Satumba (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Satumba 14, 2027

Talata · Mako na 13 bayan Fentekos · Sauti na 3

Bukukuwa da waliyyai

Beginning of the Indiction (that is, the New Year)

Azumi

Babu azumi

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Addu’ar yamma: karatu

Ish 61:1–9

1Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina, domin Ubangiji ya shafe ni domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta. Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci, don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu 2don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu, don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki, 3in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona, in maido musu rawani mai kyau a maimako na toka, man murna a maimako na makoki, da kuma rigar yabo a maimako na ruhun fid da zuciya. Za a ce da su itatuwan oak na adalci, shukin Ubangiji don bayyana darajarsa. 4Za su sāke gina kufai na dā su raya wurare da aka lalace tun da daɗewa; za su sabunta biranen da aka rurrushe da aka lalace tun zamanai masu yawa da suka wuce. 5Baƙi za su yi kiwon garkunanki; baƙi za su yi miki noman gonaki da gonakin inabinki. 6Za a kuma kira ku firistocin Ubangiji, za a kira ku masu hidimar Allahnmu. Za ku ci wadatar waɗansu al’ummai, kuma a cikin dukiyarsu za ku yi taƙama. 7A maimakon kunyarsu mutanena za su sami rabi riɓi biyu, a maimakon wulaƙanci za su yi farin ciki cikin gādonsu; ta haka za su gāji rabo riɓi biyu a ƙasarsu, da kuma madawwamin farin ciki zai zama nasu. 8“Gama ni, Ubangiji, ina ƙaunar adalci; na ƙi fashi da aikata laifi. Cikin adalcina zan sāka musu in kuma yi madawwamin alkawari da su. 9Za a san da zuriyarsu a cikin al’ummai ’ya’yansu kuma a cikin mutane. Dukan waɗanda suka gan su za su san cewa su mutane ne da Ubangiji ya sa wa albarka.”

Addu’ar yamma: karatu

Fir 26:3–12, 14–17, 19–20, 22, 33, 23–25

3“ ‘In kuka kiyaye farillaina, kuka yi biyayya da umarnaina, 4zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu ’ya’yansu. 5Masussukanku za su ci gaba har lokacin girbin inabi, girbin inabi kuma zai ci gaba har lokacin shuki, za ku kuma ci duk abincin da kuke so cikin salama a ƙasarku. 6“ ‘Zan ba ku salama a ƙasar, za ku kuwa kwanta, kuma babu wani da zai tsorata ku. Zan kori mugayen namun jeji daga ƙasar, takobi kuma ba zai ratsa cikin ƙasarku ba. 7Za ku kori abokan gābanku, za su kuwa fāɗi a kaifin takobi a gabanku. 8Mutanenku biyar za su kori mutum ɗari, mutanenku ɗari kuma za su kori mutane dubu goma, abokan gābanku kuma za su fāɗi a kaifin takobi a gabanku. 9“ ‘Zan dube ku da idon rahama, in kuma sa ku riɓaɓɓanya ku kuma ƙaru, zan kiyaye alkawarina da ku. 10Za ku ci gaba da cin girbin bara, har ku fitar da shi don ku sami wurin saboda sabo. 11Zan kafa wurin zamana a cikinku, ba zan kuma yi ƙyamarku ba. 12Zan yi tafiya a cikinki in kuma zama Allahnku, za ku kuwa zama mutanena. 14“ ‘Amma in za ku kasa kunne gare ni, ku kuma aikata dukan waɗannan umarnai, 15in kuka kuma ƙi farillaina, kuka yi ƙyamar dokokina, kuka kuma kāsa kiyaye umarnaina, har kuka karya alkawarina, 16to, zan yi muku wannan. Zan kawo muku abin bantsoro, cututtuka da zazzaɓin da zai lalatar da idonku, yă kuma sa ranku a wahala. Za ku shuka iri a banza, domin abokan gābanku ne za su ci. 17Zan yi gāba da ku har abokan gābanku su ci ku a yaƙi, su waɗanda suke ƙinku za su yi mulki a kanku, za ku gudu ba tare da wani yana korinku ba. 19Zan karya ikonku wanda kuke fariya da shi, in hana ruwan sama, ƙasa kuma tă zama kamar tagulla. 20Ƙarfinku zai ƙare a banza domin ƙasarku ba za tă ba da hatsi ba, balle itatuwan ƙasar su ba da ’ya’ya. 22Zan aika da mugayen namun jeji a kanku, za su kuwa kashe ’ya’yanku, su hallaka shanunku, su rage yawanku, ku zama kaɗan. Wannan zai sa a rasa mutane a kan hanyoyinku. 33Zan watsar da ku cikin al’ummai, in kuma ja takobina in kore ku. Ƙasarku za tă zama kufai, biranenku kuma su zama kango. 23“ ‘In duk da waɗannan abubuwa, ba ku yarda da gyaran da nake yi muku ba, kuka ci gaba da yin adawa da ni, 24zan yi adawa da ku, zan kuma aukar muku saboda zunubanku har sau bakwai. 25Zan kawo takobi a kanku don in yi ramuwa saboda karya alkawarin da kuka yi. Sa’ad da kuka janye zuwa cikin biranenku, zan aika da annoba a cikinku, za a kuwa ba da ku ga hannun abokan gāba.

Addu’ar yamma: karatu

Ba ya cikin wannan fassara

Wasiƙa (domin Sabuwar Shekarar ikkilisiya)

1Tim 2:1–7

1Da farko dai, ina gargaɗe ku cewa a yi roƙe-roƙe, ana addu’o’i, ana yin addu’a a madadin waɗansu da kuma a yi godiya saboda kowane mutum 2da sarakuna da dukan masu mulki, domin mu zauna lafiya, rai kuma kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa. 3Wannan yana da kyau, yakan kuma gamshi Allah Mai Cetonmu, 4wanda yake so dukan mutane su sami ceto su kuma zo ga sanin gaskiya. 5Gama Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya tsakanin Allah da mutane, shi ne kuwa Kiristi Yesu, 6wanda ya ba da kansa fansa domin dukan mutane, shaidar da aka bayar a daidai lokaci. 7Don haka ne aka sa ni mai wa’azi, da manzo kuma, gaskiya nake faɗa, ba ƙarya ba, na kuma zama malami mai koya wa al’ummai al’amarin bangaskiya da kuma na gaskiya.

Wasiƙa (domin Waliyyi Siman)

Kol 3:12–16

12Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa. 13Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku. 14Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya. 15Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya. 16Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah.

Bishara (domin Sabuwar Shekarar ikkilisiya)

Luk 4:16–22

16Ya tafi Nazaret, inda aka yi renonsa. A ranar Asabbaci kuma, ya shiga majami’a kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe don yă yi karatu. 17Aka kuwa ba shi naɗaɗɗen littafin annabi Ishaya. Da ya buɗe, sai ya sami wurin da aka rubuta, 18“Ruhun Ubangiji yana kaina, domin ya shafe ni, in yi wa matalauta wa’azin bishara. Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku, in kuma buɗe idanun makafi, in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne. 19In yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji.” 20Sai ya naɗe naɗaɗɗen littafin ya mayar wa mai hidimar, ya kuma zauna. Dukan idanun waɗanda suke a majami’ar, suka koma a kansa. 21Sai ya fara ce musu, “A yau, Nassin nan, ya cika a kunnenku.” 22Duk suka yabe shi, suka yi mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suka yi tambaya, suna cewa, “Anya, wannan ba ɗan Yusuf ba ne?”

Bishara (domin Waliyyi Siman)

Mat 11:27–30

27“Dukan kome Ubana ya danƙa mini. Ba wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban, sai dai Ɗan da kuma waɗanda Ɗan ya so yă bayyana musu shi. 28“Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Satumba 1 a kalandar ikilisiya shi ne Satumba 14 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi