Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Agusta 2027 › Agusta 29
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Agusta 29, 2027
Lahadi · Mako na 22 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Lahadi ta 22 ta lokacin yau da kullum
Lahadi · Launin ibada: kore
Karatun yini
Karatu na farko
1To, ku ji, ya Isra’ila, ku kasa kunne ga ƙa’idodi da dokokin da nake shirin koya muku. Ku bi su domin ku yi tsawon rai, ku kuma shiga ku mallaki ƙasar da Ubangiji, Allahn kakanninku yake ba ku. 2Kada ku ƙara, kada ku rage daga cikin abin da nake umarce ku. Amma ku kiyaye umarnan nan na Ubangiji Allahnku, da na ba ku. 6Ku kiyaye su, ku aikata su, gama yin haka zai tabbatar wa sauran al’ummai, kuna da hikima da ganewa. Sa’ad da al’ummai za su ji waɗannan dokoki, za su ce, “Ba shakka, wannan babbar al’umma tana da hikima da ganewa.” 7Wace al’umma ce mai girma haka wadda allolinta take kusa da su yadda Ubangiji Allahnmu yake kusa da mu a duk sa’ad da muka yi addu’a gare shi? 8Wace al’umma ce mai girma haka wadda take da ƙa’idodi da dokoki masu adalci kamar waɗannan ƙunshin dokokin da nake sa a gabanku a yau?
Zaburar amsawa
2Sai wanda ba shi da laifi kuma yana yin abin da yake daidai, wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa 3ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa, wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa, 4wanda yake ƙin mugun mutum amma yakan girmama masu tsoron Ubangiji, yakan cika alkawarinsa ko da ma ya zafe shi, 5wanda yake ba da rance ba tare da ruwa ba kuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi. Shi wanda yake yin waɗannan abubuwa ba zai taɓa jijjiguwa ba.
Karatu na biyu
17Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau. 18Ya zaɓa yă haife mu ta wurin kalmar gaskiya, domin mu zama ’ya’yan fari na dukan abin da ya halitta. 21Saboda haka, ku rabu da ƙazamin hali da kuma kowace irin mugunta ku kuma yi na’am da maganar da aka shuka a cikinku da tawali’u, wadda za tă iya cetonku. 22Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce. 27Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.
Bishara
1Farisiyawa da waɗansu malaman dokoki waɗanda suka zo daga Urushalima, suka taru kewaye da Yesu. 2Sai suka ga waɗansu daga cikin almajiransa suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta, wato, da ba a wanke ba. 3(Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci, sai sun wanke hannuwa sarai tukuna, yadda al’adun dattawa suka ce. 4Sa’ad da suka dawo daga wurin kasuwanci, dole su wanke hannu kafin su ci abinci. Sukan kuma kiyaye waɗansu al’adu da yawa, kamar wanken kwafuna, tuluna da butoci.) 5Saboda haka, Farisiyawa da malaman dokoki suka tambayi Yesu, suka ce, “Don me almajiranka ba sa bin al’adun dattawa, a maimakon haka suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta?” 6Ya amsa ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa, “ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni, amma zukatansu sun yi nesa da ni. 7A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokokin mutane ne kawai.’ 8Kun yar da umarnan Allah, kuna bin al’adun mutane.” 14Sai Yesu ya sāke kiran taron wurinsa ya ce, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimci wannan. 15Ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. Sai dai abin da ya fita daga cikin mutum ne, yake ƙazantar da shi.” 21Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina, 22kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta. 23Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”
Tsarkakan ranar
- Shan wahalar Waliyyi Yohanna Mai Baftisma
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi