Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Agusta 2027 › Agusta 26

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Agusta 26, 2027

Alhamis · Mako na 21 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Alhamis a mako na 21 na lokacin yau da kullum

Ranar mako · Launin ibada: kore

Karatun yini

Karatu na farko

1Tes 3:7–13

7Saboda haka ’yan’uwa, cikin dukan damuwarmu da tsananinmu an ƙarfafa mu game da ku saboda bangaskiyarku. 8Gama yanzu tabbatacce muna da rai, da yake kuna nan tsaye daram a cikin Ubangiji. 9Wace irin godiya ce za mu yi wa Allah saboda ku a kan dukan farin cikin da muke da shi a gaban Allahnmu ta dalilinku? 10Dare da rana muna addu’a da himma domin mu sāke ganinku, mu kuma ba ku abin da kuka rasa a bangaskiyarku. 11Yanzu bari Allahnmu da Ubanmu kansa da kuma Ubangijinmu Yesu yă shirya mana hanya mu zo wurinku. 12Ubangiji yă sa ƙaunarku ta ƙaru ta kuma yalwata ga juna da kuma ga kowa, kamar yadda tamu take muku. 13Bari yă ƙarfafa zukatanku har ku zama marasa aibi da kuma tsarkaka a gaban Allahnmu da Ubanmu sa’ad da Ubangijimmu Yesu ya dawo tare da dukan tsarkakansa.

Zaburar amsawa

Zab 90:3–4, 12–14, 17

3Ka komar da mutane zuwa ƙura, kana cewa, “Ku koma ƙura, ya ku ’ya’yan mutane.” 4Gama shekaru dubu a gabanka kamar kwana ɗaya ne da ya wuce, ko sa’a guda na dare. 12Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai, don mu sami zuciyar hikima. 13Ka ji mu, ya Ubangiji! Har yaushe zai ci gaba? Ka ji tausayin bayinka. 14Ka ƙosar da mu da safe da ƙaunarka marar ƙarewa, don mu rera don yabo, mu kuma yi murna dukan kwanakinmu. 17Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu; ka albarkaci mana aikin hannuwanmu, I, ka albarkaci aikin hannuwanmu.

Bishara

Mat 24:42–51

42“Saboda haka sai ku zauna a faɗake, gama ba ku san a wace rana ce Ubangijinku zai zo ba. 43Ku dai gane wannan, da maigida ya san ko a wane lokaci ne da dare, ɓarawo zai zo, da sai yă zauna a faɗake yă kuma hana a shiga masa gida. 44Saboda haka ku ma, sai ku zauna a faɗake, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku za tă ba. 45“Wane ne bawan nan mai aminci da kuma mai hikima, wanda maigida ya sa yă lura da bayi a cikin gidansa, yă riƙa ba su abinci a daidai lokaci? 46Zai zama wa bawan nan da kyau in maigidan ya dawo ya same shi yana yin haka. 47Gaskiya nake gaya muku, zai sa shi yă lura da dukan dukiyarsa. 48Amma in wannan bawa mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba.’ 49Sa’an nan yă fara dūkan ’yan’uwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya. 50Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba, a sa’ar kuma da bai sani ba. 51Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yă kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi