Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Agusta 2027 › Agusta 25

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Agusta 25, 2027

Laraba · Mako na 21 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Laraba a mako na 21 na lokacin yau da kullum

Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore

Waliyyi Joseph na Calasanz, firist · Tunawa da ba dole ba

Waliyyi Louis · Tunawa da ba dole ba

Karatun yini

Karatu na farko

1Tes 2:9–13

9Ba shakka kuna iya tunawa, ’yan’uwa, famarmu da kuma wahalarmu; mun yi aiki dare da rana don kada mu zama nauyi wa wani yayinda muke muku wa’azin bisharar Allah. 10Ku shaidu ne, haka ma Allah, na yadda muka yi zaman tsarki, adalci da kuma marar aibi a cikinku, ku da kuka ba da gaskiya. 11Gama kun san cewa mun bi da kowannenku yadda mahaifi yakan yi da ’ya’yansa, 12muna ƙarfafa ku, muna ta’azantar da ku, muna kuma gargaɗe ku ku yi rayuwar da za tă cancanci Allah, wanda ya kira ku zuwa mulkinsa da kuma ɗaukakarsa. 13Muna kuma gode wa Allah ba fasawa domin, sa’ad da kuka karɓi maganar Allah, wadda kuka ji daga gare mu, kun karɓe ta ba kamar maganar mutane ba, sai dai kamar yadda take, maganar Allah wadda take aiki a cikinku ku da kuka ba da gaskiya.

Zaburar amsawa

Zab 139:7–12

7Ina zan tafi daga Ruhunka? Ina zan gudu in tafi daga gabanka? 8In na haura zuwa sammai, kana a can; in na yi gado a zurfafa, kana a can. 9In na tashi a fikafikan safiya, in na sauka a gefe mai nisa na teku, 10can ma hannunka zai bishe ni, hannunka na dama zai riƙe ni gam. 11In na ce, “Tabbatacce duhu zai ɓoye ni haske kuma zai zama dare kewaye da ni,” 12duhu ma ba zai zama duhu gare ka ba; dare zai haskaka kamar rana, gama duhu ya yi kamar haske gare ka.

Bishara

Mat 23:27–32

27“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kuna kama da kaburburan da aka shafa musu farin fenti, waɗanda suna da kyan gani a waje, amma a ciki, cike suke da ƙasusuwan matattu da kuma kowane irin abu mai ƙazanta. 28Haka ku ma, a waje, a idon mutane, ku masu adalci ne, amma a ciki, cike kuke da munafunci da mugunta. 29“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan gina kaburbura don annabawa, ku kuma yi wa kaburburan mutane masu adalci ado. 30Kuna cewa, ‘Da mun kasance a zamanin kakanninmu, ai, da ba mu haɗa hannu da su muka karkashe annabawa ba.’ 31Ta haka kuna ba da shaida a kanku cewa ku zuriyar waɗanda suka karkashe annabawa ne. 32To, sai ku ci gaba ku cikasa ayyukan da kakanninku suka fara!

Tsarkakan ranar

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi