Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Agusta 2027 › Agusta 15

Kalandar Ortodoks · 2 ga Agusta (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Agusta 15, 2027

Lahadi · Sauti na 7

Bukukuwa da waliyyai

Lahadi ta 8 bayan Fentekos

Azumin Barcin Uwar Allah

Azumi: da mai

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Bisharar addu’ar asuba ta 8

Yoh 20:11–18

11Maryamu kuwa ta tsaya a bakin kabarin daga waje tana kuka. Da tana cikin kuka, sai ta sunkuya ta leƙa cikin kabarin, 12sai ta ga waɗansu mala’iku biyu saye da fararen tufafi, zaune a inda dā gawar Yesu take, ɗaya wajen kai ɗayan kuma wajen ƙafafu. 13Suka tambaye ta cewa, “Mace, don me kike kuka?” Ta ce, “Sun ɗauke Ubangijina, ban kuma san inda suka ajiye shi ba.” 14Da ta faɗin haka, sai ta juya ta ga Yesu tsaye, sai dai ba tă gane cewa Yesu ne ba. 15Sai ya ce, “Mace, don me kike kuka? Wa kike nema?” Ta yi tsammani shi ne mai aikin lambun, sai ta ce, “Ranka yă daɗe, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka ajiye shi, in je in ɗauke shi.” 16Yesu ya ce mata, “Maryamu.” Sai ta juya wajensa ta ɗaga murya ta ce da Arameyanci, “ Rabboni!” (Wanda yake nufin “Malam”). 17Yesu ya ce, “Kada ki riƙe ni, gama ban riga na koma wajen Uba tukuna ba. A maimako, ki tafi wajen ’yan’uwana ki gaya musu, ‘Ina komawa wajen Ubana da Ubanku, wajen Allahna da kuma Allahnku.’ ” 18Sai Maryamu Magdalin ta wajen almajiran da labari cewa, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma gaya musu cewa ya faɗa mata waɗannan abubuwa.

Wasiƙa

1Kor 1:10–18

10Ina roƙonku ’yan’uwa, a cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, dukanku ku yarda da juna, domin kada a sami tsattsaguwa a cikinku, domin kuma ku zama ɗaya, cikakku a cikin halinku da tunaninku. 11’Yan’uwana, waɗansu daga iyalin gidan Kulos sun gaya mini cewa, akwai faɗa a cikinku. 12Abin da nake nufi shi ne, ɗaya daga cikinku na cewa, “Ni ina bin Bulus,” wani na cewa, “Ni ina bin Afollos,” wani kuma, “Ni ina bin Kefas,” har wa yau wani kuma, “Ni ina bin Kiristi.” 13Kiristi a rabe ne? Bulus ne aka gicciye dominku? An yi muku baftisma a cikin sunan Bulus ne? 14Ina godiya domin ban yi wa wani baftisma a cikinku ba, sai dai Kirisbus da Gayus kaɗai. 15Don haka, ba wanda na iya cewa an yi muku baftisma a cikin sunana. 16(I, na kuma yi wa iyalin gidan Istifanas baftisma, ban da wannan, ban tuna da wani da na yi masa baftisma ba.) 17Gama Kiristi bai aike ni yin baftisma ba, sai dai wa’azin bishara ba da kalmomin hikimar mutum ba, domin kada gicciyen Kiristi ya rasa ikonsa. 18Gama saƙon gicciye wauta ne ga waɗanda suke hallaka, amma a gare mu, mu da ake ceto, ikon Allah ne.

Bishara

Mat 14:14–22

14Da Yesu ya sauka ya kuma ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu ya kuma warkar da marasa lafiyarsu. 15Da yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuma rana ta kusa fāɗuwa. Ka sallami taron don su shiga ƙauyuka su nemi wa kansu abinci.” 16Yesu ya amsa, “Ba su bukata su tafi. Ku ku ba su wani abu su ci.” 17Suka ce, “Burodi biyar da kifi biyu ne kawai muke da su a nan.” 18Ya ce, “Ku kawo mini su a nan.” 19Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane. 20Duk suka ci suka ƙoshi, almajiran kuwa suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu. 21Yawan waɗanda suka ci, sun yi wajen maza dubu biyar, ban da mata da yara. 22Nan da nan Yesu ya sa almajiran su shiga jirgin ruwa su sha gabansa, su haye zuwa ɗayan hayin, yayinda shi kuma yă sallami taron.

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Agusta 2 a kalandar ikilisiya shi ne Agusta 15 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi