Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Agusta 2027 › Agusta 15

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Agusta 15, 2027

Lahadi · Mako na 20 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Ɗaukar Budurwa Maryamu Mai Albarka zuwa sama

Babban biki · Launin ibada: fari

Karatun yini

Karatu na farko

R Yoh 11:19–12:6, 10

19Sa’an nan aka buɗe haikalin Allah da yake a sama, kuma a cikin haikalinsa aka ga akwatin alkawarinsa. Sai kuwa ga walƙiya, ƙararraki, tsawa, girgizar ƙasa, da kuma ƙanƙara masu girma. 12:1Babbar alama mai banmamaki ta bayyana a sama, mace tana lulluɓe da rana, da kuma wata a ƙarƙashin sawunta, akwai kuma rawani mai taurari goma sha biyu a kanta. 2Tana da ciki ta kuma yi kuka mai zafi yayinda take gab da haihuwa. 3Sai wata alama ta bayyana a sama, wani babban jan maciji mai kawuna bakwai da ƙahoni goma da rawani bakwai a kan kawunansa. 4Wutsiyarsa ta share kashi ɗaya bisa uku na taurari daga sararin sama ta kuma zubar da su ƙasa. Ƙaton jan macijin ya tsaya a gaban macen wadda take gab da haihuwa, don yă cinye ɗanta nan take bayan an haife shi. 5Ta haifi ɗa, namiji, wanda zai yi mulkin dukan al’ummai da sandar ƙarfe. Aka fyauce ɗanta zuwa wurin Allah da kuma kursiyinsa. 6Sai macen ta gudu zuwa hamada zuwa inda Allah ya shirya dominta, inda za a lura da ita har kwana 1,260. 10Sa’an nan na ji babbar murya daga sama tana cewa, “Yanzu ceto da iko da mulkin Allahnmu, da kuma ikon Kiristinsa. Gama mai zargin ’yan’uwanmu, wanda yake zarginsu a gaban Allahnmu dare da rana, an jefar da shi ƙasa.

Zaburar amsawa

Zab 45:9–11, 15

9’Ya’yan sarki mata suna cikin matan da ake girmama; a hannun damarka kuwa ga amarya, sarauniya saye da ofir zinariya. 10Ki saurara, ya ke diya, ki lura ku kuma kasa kunne, Ki manta da mutanenki da gidan mahaifinki. 11Sarki ya cika da sha’awar kyanki; ki girmama shi, gama shi ne maigidanki. 15Aka bi da su cikin farin ciki da murna; suka shiga fadan sarki.

Karatu na biyu

1Kor 15:20–26

20Amma tabbatacce, an tā da Kiristi daga matattu, nunan fari kuwa cikin waɗanda suka yi barci. 21Da yake mutuwa ta zo ta wurin mutum, haka tashin matattu ma ya zo ta wurin mutum. 22Kamar yadda duka suka mutu cikin Adamu, haka duka za su rayu cikin Kiristi. 23Sai dai kowa da lokacinsa. Kiristi ne nunan fari; sa’an nan sa’ad da ya dawo; za a tā da waɗanda suke nasa. 24Sa’an nan sai ƙarshen ta zo, sa’ad da zai miƙa wa Allah Uba mulki, bayan ya hallaka dukan sarauta, mulki da iko. 25Gama dole yă yi mulki har sai ya sa dukan abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa. 26Abokin gāba na ƙarshen da za a hallaka kuwa, shi ne mutuwa.

Bishara

Luk 1:39–56

39A lokacin sai Maryamu ta shirya ta gaggauta zuwa wani gari a ƙasar tudu ta Yahudiya, 40inda ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Elizabet. 41Da Elizabet ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da yake a cikinta ya yi motsi. Elizabet kuma ta cika da Ruhu Mai Tsarki. 42Sai ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata. Mai albarka ne kuma ɗan da za ki haifa! 43Me ya sa na sami wannan tagomashi har da mahaifiyar Ubangijina za tă zo wurina? 44Da jin gaisuwarki, sai jaririn da yake cikina ya yi motsi don murna. 45Mai albarka ce wadda ta gaskata cewa abin da Ubangiji ya faɗa mata zai cika!” 46Sai Maryamu ta ce, “Raina yana ɗaukaka Ubangiji 47ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona, 48gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa. Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka, 49gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa, sunansa labudda Mai Tsarki ne. 50Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa, daga zamani zuwa zamani. 51Ya aikata manyan ayyuka da hannunsa; ya watsar da waɗanda suke masu girman kai a zurfin tunaninsu. 52Ya saukar da masu mulki daga gadajen sarautarsu amma ya ɗaukaka ƙasƙantattu. 53Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwa amma ya sallami mawadata hannu wofi. 54Ya taimaki bawansa Isra’ila, yana tunawa yă nuna jinƙai 55ga Ibrahim da zuriyarsa har abada, kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu.” 56Maryamu ta zauna da Elizabet kusan wata uku sa’an nan ta koma gida.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi