Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Agusta 2027 › Agusta 2
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Agusta 2, 2027
Litinin · Mako na 18 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Litinin a mako na 18 na lokacin yau da kullum
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore
Waliyyi Eusebius na Vercelli, bishop · Tunawa da ba dole ba
Waliyyi Peter Julian Eymard, firist · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
4Wata rana, baƙin da suke cikinsu, suka fara kwaɗayin waɗansu abinci, har suka sa Isra’ilawa suka fara kuka, suna cewa, “Da mun sami nama mun ci mana! 5Mun tuna da kifin da muka ci kyauta a Masar, haka ma kayan lambu irin su kukumba, guna, safa, albasa da kuma tafarnuwa. 6Amma ga shi yanzu ba mu da wani abin marmari; in ba wannan Manna ba!” 7Manna kuwa kamar tsabar riɗi take, kamanninta kuma kamar ƙaro ne. 8Mutane sukan fita su tattara ta, su niƙa a dutsen niƙa, ko kuwa su daka a turmi. Su dafa, ko su yi waina da ita. Ɗanɗanonta yakan yi kamar abin da aka yi da man zaitun. 9Sa’ad da raɓa tana saukowa da dad dare a kan sansani, Manna ma takan sauko. 10Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko’ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar tentinsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai, sai Musa ya damu. 11Sai ya ce wa Ubangiji, “Me ya sa ka kawo wannan damuwar a kan bawanka? Me na yi da ya ɓata maka rai har ka ɗora dukan nauyin mutanen nan a kaina? 12Ni ne na yi cikin dukan mutanen nan? Ni ne na haife su? To, me ya sa ka ce in ɗauke su a ƙirjina kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka yi alkawari da rantsuwa za ka ba wa kakanninsu? 13Ina ne zan sami nama in waɗannan mutane? Sun dinga yin mini kuka suna cewa ‘Ka ba mu nama mu ci!’ 14Ba zan iya ɗaukan dukan mutanen nan ni kaɗai ba, nauyin ya yi mini yawa. 15In haka za ka yi da ni, ka kashe ni yanzu, in na sami tagomashi daga gare ka, kada ka bar ni in rayu in ga wannan baƙin ciki.”
Zaburar amsawa
11“Amma mutanena ba su saurare ni ba; Isra’ila bai miƙa kansa gare ni ba. 12Saboda haka na ba da su ga zukatansu da suka taurare don su bi dabararsu. 13“A ce mutanena za su saurare ni, a ce Isra’ila zai bi hanyoyina, 14da nan da nan sai in rinjayi abokan gābansu in kuma juye hannuna a kan maƙiyansu! 15Waɗanda suke ƙin Ubangiji za su fāɗi a gabansa da rawar jiki, hukuncinsu kuma zai dawwama har abada. 16Amma za a ciyar da ku da alkama mafi kyau; da zuma daga dutsen da zai ƙosar da ku.”
Bishara
13Sa’ad da Yesu ya ji abin da ya faru, sai ya shiga jirgin ruwa ya janye shi kaɗai zuwa wani wuri inda ba kowa. Da jin haka, taron mutane suka bi shi da ƙafa daga garuruwa. 14Da Yesu ya sauka ya kuma ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu ya kuma warkar da marasa lafiyarsu. 15Da yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuma rana ta kusa fāɗuwa. Ka sallami taron don su shiga ƙauyuka su nemi wa kansu abinci.” 16Yesu ya amsa, “Ba su bukata su tafi. Ku ku ba su wani abu su ci.” 17Suka ce, “Burodi biyar da kifi biyu ne kawai muke da su a nan.” 18Ya ce, “Ku kawo mini su a nan.” 19Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane. 20Duk suka ci suka ƙoshi, almajiran kuwa suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu. 21Yawan waɗanda suka ci, sun yi wajen maza dubu biyar, ban da mata da yara.
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Eusebius na Vercelli, bishop
- Waliyyi Peter Julian Eymard, firist
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi