Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Yuli 2027 › Yuli 17
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Yuli 17, 2027
Asabar · Mako na 15 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Asabar a mako na 15 na lokacin yau da kullum
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore
Tunawa da Budurwa Maryamu Mai Albarka a ranar Asabar · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
37Isra’ilawa suka kama tafiya daga Rameses zuwa Sukkot. Akwai maza dubu ɗari shida da suke tafiya da ƙafa, ban da mata da yara. 38Waɗansu mutane da yawa da ba Isra’ilawa ba, suka haura tare da su, da garkunan shanu, da na tumaki da awaki. 39Suka toya burodi marar yisti da garin da aka kwaɓa wanda suka kawo daga Masar. Garin da aka kwaɓan ba shi da yisti, domin an kore su daga Masar, ba su kuwa sami damar shirya wa kansu abinci ba. 40Zaman da Isra’ilawa suka yi a Masar, ya kai shekara 430. 41A ranar da shekara 430 ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan ɓangare-ɓangare na mutanen Ubangiji suka bar Masar. 42Gama Ubangiji ya yi tsaro a wannan dare, domin yă fitar da su daga Masar, a wannan dare, dole dukan Isra’ilawa su yi tsaro, don su girmama Ubangiji, cikin dukan tsararraki masu zuwa.
Zaburar amsawa
1Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi. Ƙaunarsa madawwamiya ce. 23Shi wanda ya tuna da mu cikin ƙasƙancinmu Ƙaunarsa madawwamiya ce. 24Ya kuma ’yantar da mu daga abokan gābanmu, Ƙaunarsa madawwamiya ce. 10Gare shi wanda ya kashe ’ya’yan fari Masar Ƙaunarsa madawwamiya ce. 11Ya kuma fitar da Isra’ila daga cikinsu Ƙaunarsa madawwamiya ce. 12Da hannu mai ƙarfi da hannu mai iko; Ƙaunarsa madawwamiya ce. 13Gare shi wanda ya raba Jan Teku biyu Ƙaunarsa madawwamiya ce. 14Ya kawo Isra’ila ta tsakiyarsa, Ƙaunarsa madawwamiya ce. 15Amma ya share Fir’auna da mayaƙansa cikin Jan Teku; Ƙaunarsa madawwamiya ce.
Bishara
14Amma Farisiyawa suka fita suka ƙulla shawara yadda za su kashe Yesu. 15Da ya gane wannan, sai Yesu ya janye daga wurin. Da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da dukan masu ciwonsu, 16yana jan musu kunne kada su faɗa wa kowa akan ko shi wane ne. 17Wannan kuwa domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya ne cewa, 18“Ga bawana da na zaɓa, ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi; zan sa Ruhuna a kansa, zai kuma yi shelar adalci ga al’ummai. 19Ba zai yi faɗa ko yă ɗaga murya ba, ba kuwa wanda zai ji muryarsa a kan tituna. 20Kyauron da ya tanƙwasa ba zai karye shi ba. Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba, sai ya jagoranci adalci zuwa ga nasara. 21Cikin sunansa al’ummai za su dogara.”
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi