Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Yuni 2027 › Yuni 23

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Yuni 23, 2027

Laraba · Mako na 12 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Laraba a mako na 12 na lokacin yau da kullum

Ranar mako · Launin ibada: kore

Karatun yini

Karatu na farko

Far 15:1–12, 17–18

1Bayan wannan, maganar Ubangiji ta zo wa Abram cikin mafarki cewa, “Kada ka ji tsoro, Abram. Ni ne garkuwarka, kuma ladanka zai zama mai girma.” 2Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mene ne za ka ba ni, ganin cewa ba na haihuwa, wanda kuma zai gāji gādon gidana shi ne Eliyezer mutumin Damaskus?” 3Abram ya kuma ce, “Ga shi ba ka ba ni ɗa ba, don haka bawan da aka haifa a gidana ne zai zama magājina.” 4Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, “Wannan mutum ba zai zama magājinka ba, ɗa da yake zuwa daga jikinka ne zai zama magājinka.” 5Sai Ubangiji ya fito da kai shi waje ya ce, “Ka dubi sammai ka kuma ƙirga taurari, in har za ka iya ƙirga su.” Sa’an nan ya ce masa, “Haka zuriyarka za tă zama.” 6Abram ya gaskata, Ubangiji kuma ya lasafta shi adalci ga Abram. 7Ubangiji ya kuma ce wa Abram, “Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da kai daga Ur na Kaldiyawa, domin in ba ka wannan ƙasa ka mallake ta.” 8Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, yaya zan san cewa zan mallake ta?” 9Saboda haka Allah ya ce masa, “Kawo mini karsana, akuya, da kuma rago kowanne yă kasance shi shekara uku ne, da kurciya da kuma ɗan tattabara.” 10Abram ya kawo waɗannan duka a gaban Allah, ya raba kowannensu a tsakiya, ya ajiye su gab da juna, amma bai tsaga tsuntsayen a tsaka ba. 11Sai tsuntsaye masu cin nama suka sauko a kan gawawwakin, amma Abram ya kore su. 12Yayinda rana tana fāɗuwa, sai Abram ya yi barci mai zurfi, sai wani duhu mai kauri mai kuma bantsoro ya rufe shi. 17Sa’ad da rana ta fāɗi, aka kuwa yi duhu, sai wata tukunya mai hayaƙi, mai harshen wuta mai ci, ta bayyana, ta kuma wuce tsakanin abubuwan nan da aka tsaga. 18A wannan rana, Ubangiji ya yi alkawari da Abram ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga kogin Masar zuwa babban kogi, Yuferites ke nan,

Zaburar amsawa

Zab 105:1–4, 6–9

1Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi. 2Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata. 3Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki; bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki. 4Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum. 6Ya ku zuriyar Ibrahim bawansa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub, zaɓaɓɓensa. 7Shi ne Ubangiji Allahnmu; kuma hukunce-hukuncensa suna a cikin dukan duniya. 8Yana tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu, 9alkawarin da ya yi da Ibrahim, rantsuwar da ya yi wa Ishaku.

Bishara

Mat 7:15–20

15“Ku yi hankali da annabawan ƙarya. Sukan zo muku da kamannin tumaki, amma daga ciki mugayen kyarketai ne. 16Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya? 17Haka ma kowane itace mai kyau yakan ba da ’ya’ya masu kyau, kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. 18Itace mai kyau ba ya ba da munanan ’ya’ya, haka kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. 19Duk itacen da ba ya ba da ’ya’ya masu kyau sai a sare shi a jefa cikin wuta. 20Ta haka, ta wurin aikinsu za ku gane su.”

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi