Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Yuni 2027 › Yuni 11

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Yuni 11, 2027

Juma’a · Mako na 10 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Juma’a a mako na 10 na lokacin yau da kullum

Tunawa · Launin ibada: ja

Waliyyi Barnabas, manzo · Tunawa

Azumi da tuba

Ranar tuba

Kowace Juma’a ranar tuba ce; kowace taron bishop-bishop yana tsara yadda ake kiyaye ta: kamewa daga nama ko wani aikin tuba. Azumi ya wajaba daga shekara 18 zuwa 59, kamewa daga shekara 14.

Karatun yini

Karatu na farko

Ayy M 11:21–26; 13:1–3

21Hannun Ubangiji kuwa yana tare da su, mutane da yawan gaske kuwa suka gaskata suka juya ga Ubangiji. 22Labari wannan abu ya kai kunnuwan ikkilisiya a Urushalima, sai suka aiki Barnabas zuwa Antiyok. 23Da ya iso ya kuma ga tabbacin alherin Allah, sai ya yi farin ciki ya kuma ƙarfafa su duka su tsaya da gaskiya cikin Ubangiji da dukan zukatansu. 24Mutum ne nagari, cike da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, mutane masu yawan gaske kuwa suka juya ga Ubangiji. 25Sa’an nan Barnabas ya tafi Tarshish don yă nemi Shawulu, 26sa’ad da ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antiyok. Ta haka shekara guda cur Barnabas da Shawulu suka yi suna taruwa da ikkilisiya, suka kuma koya wa mutane masu yawan gaske. A Antiyok ne aka fara kiran almajirai da suna Kirista. 13:1A ikkilisiyar da take a Antiyok akwai waɗansu annabawa da malamai. Barnabas, Siman wanda ake kira Baƙi, Lusiyus mutumin Sairin, Manayen (wanda aka goya tare da Hiridus mai mulki), da kuma Shawulu. 2Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnabas da Shawulu domin aikin da na kira su.” 3Saboda haka bayan suka yi azumi da addu’a, sai suka ɗibiya musu hannuwansu a kansu suka sallame su.

Zaburar amsawa

Zab 116:10–11, 15–18

10Na gaskata, saboda haka na ce, “An azabtar da ni ƙwarai.” 11Kuma cikin rikicewana na ce, “Dukan mutane maƙaryata ne.” 15Abu mai daraja a gaban Ubangiji shi ne mutuwar tsarkakansa. 16Ya Ubangiji, da gaske ni bawanka ne; ni bawanka ne, ɗan baiwarka; ka ’yantar da ni daga sarƙoƙi. 17Zan yi hadayar godiya gare ka in kuma kira bisa sunan Ubangiji. 18Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa,

Bishara

Mat 5:27–32

27“Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’ 28Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa. 29In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. 30In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. 31“An kuma faɗa, ‘Duk wanda ya saki matarsa, dole yă ba ta takardar saki.’ 32Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne.

Tsarkakan ranar

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi