Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Yuni 2027 › Yuni 11
Kalandar Ortodoks · 29 ga Mayu (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Yuni 11, 2027
Juma’a · Mako na 6 na lokacin Ista · Sauti na 5
Bukukuwa da waliyyai
Virginmartyr Theodosia of Constantinople († 730)
Ranar azumi
Ana iya cin kifi
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Wasiƙa
1Lokacin da Afollos yake a Korint, Bulus ya bi hanyar da ta ratsa ta Asiya ya zo Afisa. A can ya sadu da waɗansu almajirai, 2sai ya tambaye, su ya ce, “Kun karɓi Ruhu Mai Tsarki sa’ad da kuka gaskata?” Suka amsa suka ce, “A’a, ba mu ma san akwai Ruhu Mai Tsarki ba.” 3Saboda haka Bulus ya yi tambaya ya ce, “To, wace baftisma aka yi muku?” Suka ce, “Baftismar Yohanna.” 4Bulus ya ce, “Ai, baftismar Yohanna, baftisma ce ta tuba. Ya ce wa mutane su gaskata a wani wanda yake zuwa bayansa, wato, Yesu.” 5Da ji wannan, sai aka yi musu baftisma a cikin sunan Ubangiji Yesu. 6Da Bulus ya ɗibiya musu hannuwansa, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka musu, suka kuwa yi magana da harsuna, suka kuma yi annabci. 7Mutane kuwa su wajen mutum goma sha biyu ne. 8Bulus ya shiga majami’a ya yi magana gabagadi a can na watanni uku, yana muhawwara yana kuma rinjayarsu game da mulkin Allah.
Bishara
1“Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri. 3In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake. 4Ai, kun san hanyar zuwa inda za ni.” 5Sai Toma ya ce masa, “Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, to, ta yaya za mu san hanyar?” 6Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina. 7Da kun san ni, da za ku san Ubana ma. Daga yanzu, kun san shi kun kuma gan shi.” 8Filibus ya ce, “Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan kuwa zai biya bukatarmu.” 9Yesu ya amsa ya ce, “Ba san ni ba, Filibus, duk da daɗewan nan da na yi tare da ku? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Ka nuna mana Uban’? 10Ba ka gaskata cewa ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina ba? Kalmomin da nake gaya muku ba na kaina ba ne. Ai, Uban da yake raye a cikina ne yake aikinsa. 11Ku gaskata ni sa’ad da na ce ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina. Ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan banmamakin su kansu.
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Mayu 29 a kalandar ikilisiya shi ne Yuni 11 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi