Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Mayu 2027 › Mayu 25

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Mayu 25, 2027

Talata · Mako na 8 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Talata a mako na 8 na lokacin yau da kullum

Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore

Waliyyi Bede Mai Daraja, firist kuma malamin Ikkilisiya · Tunawa da ba dole ba

Waliyyi Gregory na VII, Fafaroma · Tunawa da ba dole ba

Waliyya Mary Magdalene de’ Pazzi, budurwa · Tunawa da ba dole ba

Karatun yini

Karatu na farko

Ba ya cikin wannan fassara

Zaburar amsawa

Zab 50:5–8, 14, 23

5“Ku tattara mini shafaffuna, waɗanda suka yi alkawari da ni ta wurin hadaya.” 6Sammai kuwa sun yi shelar adalcinsa gama Allah kansa alƙali ne. Sela 7“Ku ji, ya mutanena, zan kuwa yi magana, Ya Isra’ila, zan kuwa ba da shaida a kanku. Ni ne Allah, Allahnku. 8Ba na tsawata muku saboda hadayunku ko kuwa hadayunku na ƙonawa, waɗanda kuka taɓa kawo a gabana. 14“Ku miƙa hadayar godiya ga Allah, ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka, 23Shi wanda ya miƙa hadayun godiya yakan girmama ni, ya kuma shirya hanya saboda in nuna masa ceton Allah.”

Bishara

Mar 10:28–31

28Bitrus ya ce, “Mun bar kome domin mu bi ka!” 29Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko ’yan’uwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ’ya’ya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara, 30sa’an nan yă kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da ’yan’uwa mata, da ’yan’uwa maza, da uwaye, da ’ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma yă sami rai madawwami. 31Amma da yawa da suke na farko, za su zama na ƙarshe, na ƙarshe kuma, za su zama na farko.”

Tsarkakan ranar

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi