Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Mayu 2027 › Mayu 12
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Mayu 12, 2027
Laraba · Mako na 7 na lokacin Ista
Bukukuwa da waliyyai
Laraba a mako na 7 na lokacin Ista
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: fari
Waliyyi Pancras, shahidi · Tunawa da ba dole ba
Waliyyi Nereus da Waliyyi Achilleus, shahidai · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
28Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa. 29Na san cewa bayan na tafi, mugayen kyarketai za su shigo cikinku ba za su kuwa ƙyale garken ba. 30Ko cikinku ma mutane za su taso su karkatar da gaskiya don su jawo wa kansu almajirai. 31Saboda haka ku zauna a faɗake! Ku tuna cewa shekara uku, dare da rana ban taɓa fasa yin wa kowannenku gargaɗi ba, har da hawaye. 32“To, yanzu na danƙa ku ga Allah da kuma ga maganar alherinsa, wadda za tă iya gina ku ta kuma ba ku gādo a cikin dukan waɗanda aka tsarkake. 33Ban yi ƙyashin azurfa ko zinariya ko tufafin kowa ba. 34Ku kanku kun san cewa hannuwan nan nawa sun biya mini bukatuna da kuma na abokan aikina. 35Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tuƙuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ” 36Da ya faɗi haka, ya durƙusa tare da dukansu ya yi addu’a. 37Sai dukansu suka yi kuka suka rungume shi, suka kuma yi masa sumba. 38Abin da ya fi sa su baƙin ciki shi ne maganarsa da ya ce, ba za su ƙara ganin fuskarsa ba. Sai suka raka shi zuwa wajen jirgin ruwa.
Zaburar amsawa
28Ka bayyana ikonka, ya Allah; ka nuna ƙarfinka, ya Allah, kamar yadda ka yi a dā. 29Saboda haikalinka a Urushalima sarakuna za su kawo maka kyautai. 32Ku rera wa Allah, ya masarautan duniya, ku rera yabo ga Ubangiji, Sela 33gare shi wanda yake hawan daɗaɗɗen sararin sama, wanda yake tsawa da babbar murya. 34Ku yi shelar ikon Allah, wanda ɗaukakarsa take a bisa Isra’ila, wanda ikonsa yake a cikin sarari. 35Kai mai banmamaki ne, ya Allah, cikin wurinka mai tsarki; Allah na Isra’ila yakan ba da iko da kuma ƙarfi ga mutanensa. Yabo ya tabbata ga Allah!
Bishara
11Ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai Tsarki, ka kiyaye su ta wurin ikon sunanka, sunan da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya. 12Yayinda nake tare da su, na kāre su na kuma kiyaye su ta wurin sunan nan da ka ba ni. Ba ko ɗayan da ya ɓace, sai dai wannan da aka ƙaddara zuwa ga hallaka don Nassi yă cika. 13“Yanzu ina zuwa wurinka, sai dai na faɗi waɗannan abubuwa ne tun ina a duniya domin farin ciki yă zama cikakke a cikinsu. 14Na gaya musu maganarka duniya kuwa ta ƙi su, don su ba na duniya ba ne yadda ni ma ba na duniya ba ne. 15Ba addu’ata ba ce ka ɗauke su daga duniya ba, sai dai ka kāre su daga mugun nan. 16Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 17Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya. 18Kamar yadda ka aiko ni cikin duniya, haka ni ma na aike su cikin duniya. 19Saboda su ne na tsarkake kaina, domin su ma a tsarkake su da gaske.
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Pancras, shahidi
- Waliyyi Nereus da Waliyyi Achilleus, shahidai
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi