Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Afirilu 2027 › Afirilu 9
Kalandar Ortodoks · 27 ga Maris (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Afirilu 9, 2027
Juma’a · Mako na 4 na Babban Azumi · Sauti na 3
Bukukuwa da waliyyai
Martyr Matrona of Thessalonica (3rd-4th C)
Babban Azumi
Azumi mai tsanani (busasshen abinci: burodi, ganye, ’ya’yan itace)
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Sa’a ta 6
13Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane sun zo kusa da ni da bakinsu suka kuma girmama ni da leɓunansu, amma zukatansu suna nesa daga gare ni. Sujadar da suke mini cike take da dokokin da mutane suka koyar. 14Saboda haka zan firgita waɗannan mutane sau ɗaya da abubuwan banmamaki a kan abubuwan banmamaki; hikimar masu hikima za tă lalace, azancin masu azanci zai ɓace.” 15Kaiton waɗanda suke zuwa manyan zurfafa don su ɓoye shirye-shiryensu daga Ubangiji, waɗanda suke aikinsu cikin duhu su yi tunani, “Wa yake ganinmu? Wa zai sani?” 16Kuna birkitar abubuwa, sai ka ce an mayar da mai ginin tukwane ya zama yumɓu! Abin da aka yi zai ce wa wanda ya yi shi, “Ba shi ne ya yi ni ba”? Tukunya za tă iya ce wa mai ginin tukwane, “Ba ka san kome ba”? 17Cikin ɗan lokaci, za a mai da Lebanon gona mai taƙi kuma gona mai taƙi za tă zama kamar kurmi? 18A wannan rana kurame za su ji maganganun littafi, daga duruduru da duhu kuma idanun makafi za su gani. 19Masu tawali’u za su sāke yin farin ciki a cikin Ubangiji; mabukata za su yi farin ciki cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila. 20Masu zalunci za su ƙare, masu ba’a za su ɓace, kuma dukan waɗanda suke da ido don mugunta za su hallaka, 21waɗanda ta magana kawai sukan mai da mutum mai laifi, waɗanda suke kafa tarko wa mai ba da kāriya a ɗakin shari’a da shaidar ƙarya kuma su hana marar laifi samun shari’ar adalci. 22Saboda haka ga abin da Ubangiji wanda ya fanshi Ibrahim, ya ce wa gidan Yaƙub, “Ba za a ƙara kunyata Yaƙub ba; fuskokinsu kuma ba za su ƙara yanƙwanewa ba. 23Sa’ad da suka ga ’ya’yansu a tsakiyarsu, aikin hannuwansu, za su kiyaye sunana da tsarki; za su san tsarkin Mai Tsarkin nan na Yaƙub, za su kuma ji tsoron Allah na Isra’ila.
Addu’ar yamma: karatu
1Ubangiji ya ce wa Abram, “Tashi ka bar ƙasarka, da mutanenka, da iyalin mahaifinka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka. 2“Zan mai da kai al’umma mai girma, zan kuma albarkace ka; zan sa sunanka yă zama mai girma, ka kuma zama sanadin albarka. 3Zan albarkaci duk wanda ya albarkace ka, in kuma la’anci duk wanda ya la’anta ka, dukan mutanen duniya za su sami albarka ta wurinka.” 4Saboda haka Abram ya tashi yadda Ubangiji ya faɗa masa; Lot ma ya tafi tare da shi. Abram yana da shekaru 75, sa’ad da ya tashi daga Haran. 5Abram ya ɗauki matarsa Saira da Lot ɗan ɗan’uwansa, da dukan mallakar da suka tattara, da kuma mutanen da suka samu a Haran, suka kama hanya zuwa ƙasar Kan’ana. 6Abram ya ratsa ƙasar har zuwa wurin babban itace na More a Shekem. A lokacin Kan’aniyawa suna a ƙasar. 7Ubangiji ya bayyana ga Abram ya ce, “Ga zuriyarka ne zan ba da wannan ƙasa.” Saboda haka Abram ya gina bagade a can ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi.
Addu’ar yamma: karatu
15Marar azanci kan gaskata kome, amma mai la’akari kan yi tunani game da matakinsa. 16Mai hikima kan ji tsoron Ubangiji ya kuma guji mugunta, amma wawa yana da girman kai yakan yi kome da garaje. 17Mutum mai saurin fushi yakan yi ayyukan wauta, akan kuma ƙi mai son nuna wayo. 18Marar azanci kan gāji wauta, amma mai la’akari kan sami rawanin sani. 19Masu mugunta za su rusuna a gaban masu kirki, mugaye kuma za su yi haka a ƙofofin adalai. 20Maƙwabta sukan gudu daga matalauta, amma masu arziki suna da abokai da yawa. 21Duk wanda ya rena maƙwabci ya yi zunubi, amma mai albarka ne wanda yake alheri ga mabukata. 22Ba waɗanda suke ƙulla mugunta sukan kauce ba? Amma waɗanda suke ƙulla abin da yake mai kyau sukan sami ƙauna da aminci. 23Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba, amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai. 24Dukiyar masu hikima ita ce rawaninsu, amma wautar wawaye kan haifar da wauta ne kawai. 25Mashaidin gaskiya kan ceci rayuka, amma mashaidin ƙarya mai ruɗu ne. 26Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka, kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka.
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Maris 27 a kalandar ikilisiya shi ne Afirilu 9 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi