Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Maris 2027 › Maris 3

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Maris 3, 2027

Laraba · Mako na 3 na lokacin Azumi

Bukukuwa da waliyyai

Laraba a mako na 3 na lokacin Azumi

Ranar mako · Launin ibada: shunayya

Karatun yini

Karatu na farko

M Sh 4:1, 5–9

1To, ku ji, ya Isra’ila, ku kasa kunne ga ƙa’idodi da dokokin da nake shirin koya muku. Ku bi su domin ku yi tsawon rai, ku kuma shiga ku mallaki ƙasar da Ubangiji, Allahn kakanninku yake ba ku. 5Ga shi, na koya muku ƙa’idodi da dokoki, yadda Ubangiji Allahna ya umarce ni, don ku bi su a ƙasar da za ku shiga ku mallaki. 6Ku kiyaye su, ku aikata su, gama yin haka zai tabbatar wa sauran al’ummai, kuna da hikima da ganewa. Sa’ad da al’ummai za su ji waɗannan dokoki, za su ce, “Ba shakka, wannan babbar al’umma tana da hikima da ganewa.” 7Wace al’umma ce mai girma haka wadda allolinta take kusa da su yadda Ubangiji Allahnmu yake kusa da mu a duk sa’ad da muka yi addu’a gare shi? 8Wace al’umma ce mai girma haka wadda take da ƙa’idodi da dokoki masu adalci kamar waɗannan ƙunshin dokokin da nake sa a gabanku a yau? 9Ku kula, ku kuma lura da kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da idanunku suka gani, ko kuwa ku bari su fita daga zuciyarku muddin ranku. Ku koyar da su ga ’ya’yanku, da ’ya’yan ’ya’yanku.

Zaburar amsawa

Zab 147:12–13, 15–16, 19

12Ki ɗaukaka Ubangiji, ya Urushalima; ki yabi Allahnki, ya Sihiyona. 13Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinki yana kuma albarkace mutanenki a cikinki. 15Yana ba da umarninsa ga duniya; maganarsa tana tafiya da sauri. 16Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar ulu yă kuma watsar da hazo kamar toka. 19Ya bayyana maganarsa ga Yaƙub, dokokinsa da ƙa’idodinsa ga Isra’ila.

Bishara

Mat 5:17–19

17“Kada ku yi tsammani na zo ne domin in kawar da Doka ko kuma Annabawa; ban zo domin in kawar da su ba ne, sai dai domin in ciccika su. 18Gaskiya nake gaya muku, kafin sama da ƙasa sun shuɗe, babu ko ɗan wasali, babu wani ɗigo ta kowace hanya da zai ɓace daga Dokar, sai an cika kome. 19Duk wanda ya karya ɗaya daga cikin mafi ƙanƙanta na umarnan nan, ya kuma koya wa waɗansu su yi haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a mulkin sama. Amma duk wanda ya aikata, ya kuma koyar da waɗannan umarnai, za a kira shi mai girma a cikin mulkin sama.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi