Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Faburairu 2027 › Faburairu 27
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Faburairu 27, 2027
Asabar · Mako na 2 na lokacin Azumi
Bukukuwa da waliyyai
Asabar a mako na 2 na lokacin Azumi
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: shunayya
Waliyyi Gregory na Narek, shugaban masu zuhudu kuma malamin Ikkilisiya · Ambato
Karatun yini
Karatu na farko
14Ka yi kiwon mutanenka da sandarka, garken gādonka, wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi, a ƙasa mai kyau ta kiwo, bari su yi kiwo a Bashan da Gileyad kamar a kwanakin dā. 15“Kamar a kwanakin da kuka fito daga Masar, zan nuna musu al’ajabaina.” 18Wane ne Allah kamar ka, wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu? Ba ka zama mai fushi har abada amma kana marmari ka nuna jinƙai. 19Za ka sāke jin tausayinmu; za ka tattake zunubanmu a ƙarƙashin sawunka ka kuma tura dukan kurakuranmu zuwa cikin zurfafan teku. 20Za ka yi wa Yaƙub aminci, ka kuma nuna jinƙai ga Ibrahim, kamar yadda ka yi alkawari da rantsuwa ga kakanninmu tun a kwanankin dā.
Zaburar amsawa
1Ta Dawuda. Yabi Ubangiji, ya raina; dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki. 2Yabi Ubangiji, ya raina, kada kuma ka manta dukan alheransa, 3wanda yake gafarta dukan zunubai yake kuma warkar da dukan cututtuka, 4wanda ya fanshi ranka daga rami ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi, 9Ba zai yi ta zargi ba ba kuwa zai yi ta jin fushi har abada ba; 10ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu. 11Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya, haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa; 12kamar yadda gabas yake daga yamma, haka ya cire laifofinmu daga gare mu.
Bishara
1Yanzu fa, masu karɓar haraji da “masu zunubi” duka suna taruwa don jin koyarwar Yesu. 2Amma Farisiyawa da malaman dokoki suka yi gunaguni, suna cewa, “Wannan mutum yana karɓan ‘masu zunubi,’ kuma yana ci tare da su.” 3Sai Yesu ya faɗa musu wannan misali ya ce, 11Yesu ya ci gaba da cewa, “Akwai wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza. 12Ƙaramin ya ce wa mahaifinsu, ‘Baba, ba ni rabon gādona.’ Sai mahaifin ya raba musu dukiyarsa. 13“Bayan ’yan kwanaki, sai ƙaramin ɗan ya tattara kayansa duk, ya tashi ya tafi wata ƙasa mai nisa. A can, ya ɓatar da dukiyarsa duka a rayuwar banza. 14Bayan ya ɓatar da kome, sai ga muguwar yunwa a dukan ƙasar, har ya shiga rashi. 15Sai ya je ya sami aiki a wurin wani mutumin ƙasar, wanda ya aike shi a gonakinsa, ya yi kiwon aladu. 16Ya yi marmarin cin dusan da aladun suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu. 17“Da hankalinsa ya dawo, sai ya ce, ‘Kai, bayin mahaifina guda nawa ne, da suke da abinci fiye da isashe, ni kuma ina nan, zan mutu don yunwa! 18Zan tashi in koma wurin mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. 19Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin bayinka.” ’ 20Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa. “Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba. 21“Sai ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba.’ 22“Amma mahaifin ya ce wa bayinsa, ‘Maza! Ku kawo riga mafi kyau ku sa masa. Ku sa zobe a yatsarsa, da takalma kuma a ƙafafunsa. 23Ku kawo ɗan saniya mai ƙiba ku yanka. Bari mu yi biki mu yi shagali. 24Gama ɗan nan nawa, da ya mutu, amma yanzu yana da rai kuma. Da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ Sai suka fara shagali. 25“Yayinda ake haka, babban ɗan yana gona. Da ya zo kusa da gida, sai ya ji ana kiɗi ana rawa. 26Sai ya kira ɗaya daga cikin bayin, ya tambaye shi abin da yake faruwa. 27Bawan ya ce, ‘Ai, ɗan’uwanka ne ya dawo, shi ne mahaifinka ya yanka ɗan saniya mai ƙiba, gama ya yi murna ya karɓi ɗansa da ya dawo gida lafiyayye, ba abin da ya same shi.’ 28“Sai yayan ya yi fushi, ya ƙi shiga gida. Sai mahaifinsa ya fita ya roƙe shi. 29Amma ya amsa wa mahaifinsa ya ce, ‘Duba! Duk waɗannan shekaru, ina yin maka aiki kamar bawa, ban taɓa maka rashin biyayya ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan akuya domin in yi shagali da abokaina ba. 30Amma da wannan ɗan naka, wanda ya ɓatar da dukiyarka a kan karuwai ya dawo, ka yanka masa ɗan saniya mai ƙiba!’ 31“Sai mahaifin ya ce masa, ‘Ɗana, kullum kana nan tare da ni, kuma duk abin da nake da shi, naka ne. 32Amma ya zama mana dole, mu yi shagali, mu yi murna, domin ɗan’uwan nan naka, da ya mutu, yanzu kuwa yana da rai, da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ ”
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Gregory na Narek, shugaban masu zuhudu kuma malamin Ikkilisiya
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi