Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Janairu 2027 › Janairu 9

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Janairu 9, 2027

Asabar · Lokacin Kirsimeti

Bukukuwa da waliyyai

Asabar bayan Bayyanuwar Ubangiji

Ranar mako · Launin ibada: fari

Karatun yini

Karatu na farko

1Yoh 4:11–18

11Abokaina ƙaunatattu, da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ya kamata mu ma mu ƙaunaci juna. 12Ba wanda ya taɓa ganin Allah; amma in muna ƙaunar juna, Allah yana raye a cikinmu, ƙaunarsa kuwa ta zama cikakkiya a cikinmu ke nan. 13Mun san cewa muna rayuwa a cikinsa shi kuma a cikinmu, domin ya ba mu Ruhunsa. 14Mun gani, mun kuma shaida cewa Uba ya aiko Ɗansa domin yă zama Mai Ceton duniya. 15Duk wanda ya yarda cewa Yesu Ɗan Allah ne, Allah yana raye a cikinsa, shi kuma a cikin Allah. 16Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana. Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa. 17Ta haka, ƙauna ta zama cikakkiya a cikinmu domin mu kasance masu ƙarfin hali a ranar shari’a, domin a wannan duniya muna kama da shi. 18Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne a cikin ƙauna.

Zaburar amsawa

Zab 72:1–2, 10–13

1Ta Solomon. Ka tanada sarki da shari’arka ta gaskiya, ya Allah, ɗan sarki da adalcinka. 2Zai shari’anta mutanenka da adalci, marasa ƙarfinka da shari’ar gaskiya. 10Sarakunan Tarshish da na bakin kogi masu nisa za su ba da gandu gare shi; sarakunan Sheba da Seba za su ba shi kyautai. 11Dukan sarakuna za su rusuna masa kuma dukan al’ummai za su bauta masa. 12Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka, marasa ƙarfin da ba su da mai taimako. 13Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata yă ceci masu bukata daga mutuwa.

Bishara

Mar 6:45–52

45Nan da nan Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su sha gabansa zuwa Betsaida, shi kuma yă sallami taron. 46Bayan ya bar su, sai ya hau kan dutse don yă yi addu’a. 47Da yamma ta yi, jirgin ruwan yana tsakiyar tafkin, Yesu kuma yana can a ƙasa shi kaɗai. 48Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su, 49amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu, 50domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata. Nan da nan ya yi magana da su ya ce, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.” 51Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki, 52gama ba su fahimci al’amarin burodin nan ba, don zuciyarsu ta taurare.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi