Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Janairu 2027 › Janairu 2

Kalandar Ortodoks · 20 ga Disamba (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Janairu 2, 2027

Asabar · Mako na 31 bayan Fentekos · Sauti na 5

Bukukuwa da waliyyai

Asabar kafin Haihuwar Kiristi

Azumin Haihuwar Kiristi

Azumi: da mai

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Wasiƙa

Kol 1:3–6

3Kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, sa’ad da muke addu’a dominku. 4Gama mun ji labarin bangaskiyarku a cikin Yesu Kiristi da kuma ƙaunar da kuke yi saboda dukan tsarkaka. 5Kuna yin haka ne kuwa domin abin da kuke bege yana a ajiye a sama. Kun riga kun ji game da wannan bege sa’ad da kuka gaskata saƙon nan na gaskiya wanda shi ne bisharar 6da ta zo muku. Ko’ina a duniya wannan bishara tana yi ta haihuwa tana kuma girma, kamar yadda take yi a cikinku tun daga ranar da kuka ji ta kuka kuma fahimci alherin Allah cikin dukan gaskiyarta.

Wasiƙa (domin Asabar kafin Haihuwar Kiristi)

Gal 3:8–12

8Nassi ya hanga cewa Allah zai kuɓutar da Al’ummai ta wurin bangaskiya, ya kuwa sanar wa Ibrahim wannan bisharar tun kafin lokaci yă yi cewa, “Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinka.” 9Saboda haka waɗanda suke da bangaskiya sun sami albarka tare da Ibrahim, mutumin bangaskiya. 10Dukan waɗanda suka dogara ga kiyaye Doka la’anannu ne, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda bai ci gaba da yi dukan abubuwan da aka rubuta a Littafin Doka ba.” 11A fili yake ba wanda zai kuɓuta a gaban Allah ta wurin Doka, domin “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.” 12Doka ba tă dangana ga bangaskiya ba; a maimakon haka, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”

Bishara

Luk 14:1–11

1Wata ranar Asabbaci, da Yesu ya shiga gidan wani sanannen Bafarisiye don cin abinci, sai mutane suka zuba masa ido da kyau. 2A nan a gabansa kuwa akwai wani mutum mai ciwon kumburin ƙafa da hannu. 3Sai Yesu ya tambayi masanan dokoki da Farisiyawa ya ce, “Daidai ne bisa ga doka, a yi warkarwa a ranar Asabbaci, ko babu?” 4Amma ba su ce kome ba. Sai ya riƙe mutumin, ya warkar da shi, sa’an nan ya sallame shi. 5Sai ya tambaye, su ya ce, “In wani a cikinku yana da ɗa, ko bijimi da ya faɗa a rijiya a ranar Asabbaci, ba za ku cire shi nan da nan ba?” 6Suka rasa abin faɗi. 7Da ya lura da yadda baƙi suna zaɓan wuraren zama masu bangirma a tebur, sai ya faɗa musu wannan misali, ya ce; 8“In wani ya gayyace ka bikin aure, kada ka zaɓi wurin zama mai bangirma, don wataƙila akwai wani da ya fi ka girma, da aka gayyata. 9In kuwa haka ne, wanda ya gayyace duk biyunku, zai zo ya ce maka, ‘Ka ba wa mutumin nan wurin zamanka.’ Ka ga, an ƙasƙantar da kai, kuma dole ka ɗauki wuri mafi ƙasƙanci. 10Amma in an gayyace ka, ɗauki wuri mafi ƙasƙanci, don in wanda ya gayyace ka ya zo, zai ce maka, ‘Ka hawo nan aboki a wuri mafi girma.’ Wannan zai ɗaukaka ka a gaban dukan ’yan’uwanka baƙi. 11Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Shi wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”

Bishara (domin Asabar kafin Haihuwar Kiristi)

Luk 13:18–29

18Sai Yesu ya yi tambaya ya ce, “Yaya mulkin Allah yake? Da me zan kwatanta shi? 19Yana kama da ƙwayar mustad, wadda wani mutum ya ɗauka, kuma ya shuka a gonarsa. Ta yi girma, ta zama itace, kuma tsuntsayen sararin sama suka huta a rassansa.” 20Ya sāke tambaya, “Da me zan kwatanta mulkin Allah? 21Yana kama da yisti wadda mace ta ɗauka, ta kwaɓa garin alkama mai yawa da shi, har sai da yistin ya gauraye kullun duka.” 22Sa’ad da Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi ta cikin garuruwan da ƙauyukan, yana koyarwa. 23Sai wani ya tambaye shi ya ce, “Ya Ubangiji, shin, wai mutane kima ne kawai za su sami ceto?” Ya ce musu, 24“Ku yi matuƙar ƙoƙari ku shiga ta matsattsiyar ƙofa, domin ina faɗa muku, mutane da yawa za su yi ƙoƙarin shiga, amma ba za su iya ba. 25Da zaran maigidan ya tashi ya rufe ƙofar, za ku tsaya a waje kuna ƙwanƙwasawa, kuna roƙo cewa, ‘Ranka yă daɗe, buɗe mana ƙofa.’ “Amma shi zai amma ya ce, ‘Ni ban san ku, ko inda kuka fito ba.’ 26“Sa’an nan za ku ce, ‘Haba, mu da muka ci, muka sha tare da kai, har ka yi koyarwa a cikin titi-titi namu.’ 27“Amma shi zai amma ya ce, ‘Ban san ku, ko inda kuka fito ba. Ku rabu da ni, dukan ku masu aikata mugunta!’ 28“Za a yi kuka a can, da cizon haƙora, sa’ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, da dukan annabawa a mulkin Allah, amma ku kuwa, za a jefar da ku a waje. 29Mutane za su zo daga gabas, da yamma, da kudu, da arewa, su ɗauki wuraren zamansu a bikin, a cikin mulkin Allah.

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Disamba 20 a kalandar ikilisiya shi ne Janairu 2 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi