Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Disamba 2026 › Disamba 11

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Disamba 11, 2026

Juma’a · Mako na 2 na lokacin Zuwan Ubangiji

Bukukuwa da waliyyai

Juma’a a mako na 2 na lokacin Zuwan Ubangiji

Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: shunayya

Waliyyi Damasus na I, Fafaroma · Tunawa da ba dole ba

Azumi da tuba

Ranar tuba

Kowace Juma’a ranar tuba ce; kowace taron bishop-bishop yana tsara yadda ake kiyaye ta: kamewa daga nama ko wani aikin tuba. Azumi ya wajaba daga shekara 18 zuwa 59, kamewa daga shekara 14.

Karatun yini

Karatu na farko

Ish 48:17–19

17Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya koya muku abin da ya fi muku kyau, wanda ya muku hanyar da za ku bi. 18Da a ce kawai za ku mai da hankali ga umarnaina, da salamarku ta zama kamar kogi, adalcinku kamar raƙuman teku. 19Da zuriyarku ta zama kamar yashi, ’ya’yanku kamar tsabar hatsin da ba a iya ƙidayawa; da ba za a taɓa yanke sunansu balle a hallaka su daga gabana ba.”

Zaburar amsawa

Zab 1:1–4, 6

1Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a. 2Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana. 3Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa, wanda yake ba da amfani a daidai lokaci wanda kuma ganyensa ba sa bushewa. Duk abin da yake yi, yakan yi nasara. 4Ba haka yake da mugaye ba! Su kamar yayi ne da iska take kwashewa. 6Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa, amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.

Bishara

Mat 11:16–19

16“Da me zan kwatanta wannan zamani? Suna kama da yara da suke zaune a kasuwa, suna kiran juna, suna cewa, 17“ ‘Mun yi muku busa, ba ku kuwa yi rawa ba, mun rera waƙar makoki, ba ku kuwa yi makoki ba.’ 18Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo ba ya ciye-ciye, ba ya shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ 19Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”

Tsarkakan ranar

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi