Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Disamba 2026 › Disamba 3
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Disamba 3, 2026
Alhamis · Mako na 1 na lokacin Zuwan Ubangiji
Bukukuwa da waliyyai
Alhamis a mako na 1 na lokacin Zuwan Ubangiji
Tunawa · Launin ibada: fari
Waliyyi Francis Xavier, firist · Tunawa
Karatun yini
Karatu na farko
1A wannan rana za a rera wannan waƙa a ƙasar Yahuda. Muna da birni mai ƙarfi; Allah yake ceton katanga da kuma kagarunta. 2A buɗe ƙofofi saboda al’umma mai adalci ta shiga, al’ummar da mai aminci. 3Za ka kiyaye shi da cikakken salama shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka, domin ya dogara a gare ka. 4Ku dogara ga Ubangiji, gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse. 5Yakan ƙasƙantar da waɗanda suke zama a bisa ya kawar da birni mai alfarma ƙasa; ya rusa ta har ƙasa ya jefar da ita cikin ƙura. 6Ƙafafu sukan tattake ta, ƙafafu waɗanda aka zalunta, wato, sawun matalauta.
Zaburar amsawa
1Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada. 8Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga mutum. 9Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga sarakuna. 19Buɗe mini ƙofofin adalci; zan shiga in kuma yi godiya ga Ubangiji. 20Wannan ne ƙofar Ubangiji inda adalai za su shiga. 21Zan yi maka godiya, domin ka amsa mini; ka zama mai cetona. 25Ya Ubangiji, ka cece mu; Ya Ubangiji, ka ba mu nasara. 26Mai albarka ne shi mai zuwa cikin sunan Ubangiji. Daga gidan Ubangiji muna sa muku albarka. 27Ubangiji shi ne Allah ya kuma sa haskensa ya haskaka a kanmu. Da kwanoni a hannunmu, muka shiga jerin gwanon biki ku kai su ƙahoni na bagade.
Bishara
21“Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama. 24“Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. 25Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse. 26Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. 27Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Francis Xavier, firist
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi