Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Disamba 2026 › Disamba 4

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Disamba 4, 2026

Juma’a · Mako na 1 na lokacin Zuwan Ubangiji

Bukukuwa da waliyyai

Juma’a a mako na 1 na lokacin Zuwan Ubangiji

Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: shunayya

Waliyyi John na Damaskus, firist kuma malamin Ikkilisiya · Tunawa da ba dole ba

Azumi da tuba

Ranar tuba

Kowace Juma’a ranar tuba ce; kowace taron bishop-bishop yana tsara yadda ake kiyaye ta: kamewa daga nama ko wani aikin tuba. Azumi ya wajaba daga shekara 18 zuwa 59, kamewa daga shekara 14.

Karatun yini

Karatu na farko

Ish 29:17–24

17Cikin ɗan lokaci, za a mai da Lebanon gona mai taƙi kuma gona mai taƙi za tă zama kamar kurmi? 18A wannan rana kurame za su ji maganganun littafi, daga duruduru da duhu kuma idanun makafi za su gani. 19Masu tawali’u za su sāke yin farin ciki a cikin Ubangiji; mabukata za su yi farin ciki cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila. 20Masu zalunci za su ƙare, masu ba’a za su ɓace, kuma dukan waɗanda suke da ido don mugunta za su hallaka, 21waɗanda ta magana kawai sukan mai da mutum mai laifi, waɗanda suke kafa tarko wa mai ba da kāriya a ɗakin shari’a da shaidar ƙarya kuma su hana marar laifi samun shari’ar adalci. 22Saboda haka ga abin da Ubangiji wanda ya fanshi Ibrahim, ya ce wa gidan Yaƙub, “Ba za a ƙara kunyata Yaƙub ba; fuskokinsu kuma ba za su ƙara yanƙwanewa ba. 23Sa’ad da suka ga ’ya’yansu a tsakiyarsu, aikin hannuwansu, za su kiyaye sunana da tsarki; za su san tsarkin Mai Tsarkin nan na Yaƙub, za su kuma ji tsoron Allah na Isra’ila. 24Su da suke marasa azanci a ruhu za su sami fahimtar; waɗanda suke gunaguni za su yarda da koyarwa.”

Zaburar amsawa

Zab 27:1, 4, 13–14

1Ta Dawuda. Ubangiji ne haskena da cetona, wa zan ji tsoro? Ubangiji ne mafakar raina, wane ne zan ji tsoro? 4Abu guda na roƙi Ubangiji, wannan shi ne na nema, cewa in zauna a gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, in dubi kyan Ubangiji in kuma neme shi a cikin haikalinsa. 13Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewa zan ga alherin Ubangiji; a ƙasar masu rai. 14Ka dogara ga Ubangiji, ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya ka kuma dogara ga Ubangiji.

Bishara

Mat 9:27–31

27Da Yesu ya fita daga can, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna kira, suna cewa, “Ka yi mana jinƙai, Ɗan Dawuda!” 28Da ya shiga cikin gida, sai makafin nan suka zo wurinsa, ya kuma tambaye su, “Kun gaskata cewa ina iya yin wannan?” Suka amsa suka ce, “I, Ubangiji.” 29Sa’an nan ya taɓa idanunsu ya ce, “Bisa ga bangaskiyarku a yi muku haka”; 30sai idanunsu suka buɗe. Yesu ya gargaɗe su sosai ya ce, “Ku lura kada wani yă san wani abu game da wannan.” 31Amma suka fita suka yi ta baza labari game da shi ko’ina a wannan yankin.

Tsarkakan ranar

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi