Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Nuwamba 2026 › Nuwamba 21

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Nuwamba 21, 2026

Asabar · Mako na 33 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Asabar a mako na 33 na lokacin yau da kullum

Tunawa · Launin ibada: fari

Miƙa Budurwa Maryamu Mai Albarka a haikali · Tunawa

Karatun yini

Karatu na farko

R Yoh 11:4–12

4Waɗannan su ne itatuwan zaitun biyu da kuma alkukai biyu da suke tsaye a gaban Ubangijin duniya. 5Duk wanda ya yi ƙoƙari yin musu lahani, wuta za tă fito daga bakunansu ta cinye abokan gābansu. Haka ne duk mai niyyar yin musu lahani zai mutu. 6Waɗannan mutane suna da iko su kulle sararin sama don kada a yi ruwan sama a lokacin da suke annabci; suna kuma da iko su juye ruwaye su zama jini su kuma bugi duniya da kowace irin annoba a duk lokacin da suke so. 7To, da suka gama shaidarsu, dabbar da takan fito daga Abis za tă kai musu hari, tă kuwa sha ƙarfinsu tă kuma kashe su. 8Gawawwakinsu za su kasance a kwance a titin babban birni, wanda a misalce ake kira Sodom da Masar, inda kuma aka gicciye Ubangijinsu. 9Kwana uku da rabi mutane daga kowace jama’a, kabila, harshe da kuma al’umma za su yi ta kallon gawawwakinsu su kuma ƙi binne su. 10Mazaunan duniya za su ƙyaface su kuma yi biki ta wurin aika kyautai wa juna, domin waɗannan annabawan nan biyu ne suka azabtar da mazaunan duniya. 11Amma bayan kwana uku da rabi ɗin numfashin rai daga Allah ya shige su, suka kuwa tashi tsaye, tsoro kuma ya kama waɗanda suka gan su. 12Sai suka ji wata babbar murya daga sama tana ce musu, “Ku hauro nan.” Suka kuwa haura zuwa sama cikin girgije, yayinda abokan gābansu suna kallo.

Zaburar amsawa

Zab 144:1–2, 9–10

1Ta Dawuda. Yabo ya tabbata ga Ubangiji dutsena, wanda ya horar da hannuwana don yaƙi, yatsotsina don faɗa. 2Shi ne Allah mai ƙaunata da kuma kagarata, katangata da mai cetona, garkuwata, wanda nake neman mafaka daga gare shi, wanda ya sa mutane a ƙarƙashina. 9Zan rera sabuwar waƙa gare ka, ya Allah; a kan molo mai tsirkiya goma zan yi maka kiɗi, 10ga Wannan wanda yake ba wa sarakuna nasara, wanda ya cece bawansa Dawuda. Daga takobin kisa.

Bishara

Luk 20:27–40

27Waɗansu Sadukiyawa da suke cewa, ba tashin matattu, suka zo wurin Yesu da tambaya cewa, 28“Malam, Musa ya rubuta mana cewa, ‘In ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata amma ba ’ya’ya, dole mutumin ya aure gwauruwar, ya samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya.’ 29To, an yi waɗansu ’yan’uwa bakwai. Na fari ya auri wata mace, ya mutu ba ’ya’ya. 30Na biyun, 31da na ukun suka aure ta. Haka nan dukansu bakwai suka mutu babu ’ya’ya. 32A ƙarshe, ita macen ma ta mutu. 33Shin, a tashin matattu, matar wa za tă zama? Tun da su bakwan nan, sun aure ta.” 34Yesu ya amsa ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure, 35amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba. 36Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar mala’iku ne. Su ’ya’yan Allah ne, tun da su ’ya’yan tashin matattu ne. 37Amma bisa ga labari na bishiya nan, mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, ko Musa ma, ya nuna cewa, matattu suna tashi. Gama ya kira Ubangiji, ‘Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yaƙub.’ 38Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai ne, gama a gare shi, duka na da rai.” 39Sai waɗansu malaman dokoki suka amsa suka ce, “Ka faɗi daidai, malam!” 40Kuma ba wanda ya sami ƙarfin halin yin masa waɗansu tambayoyi.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi A, shekarar ranakun mako II.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi