Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Nuwamba 2026 › Nuwamba 15
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Nuwamba 15, 2026
Lahadi · Mako na 33 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Lahadi ta 33 ta lokacin yau da kullum
Lahadi · Launin ibada: kore
Karatun yini
Karatu na farko
10Wa yake iya samun mace mai halin kirki? Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai. 11Mijinta yana da cikakken amincewa da ita kuma ba ya rasa wani abu mai daraja. 12Takan yi masa alheri ba mugunta ba, dukan kwanakin ranta. 13Takan zaɓi ulu da lilin ta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki. 19Da hannunta take riƙe abin kaɗi ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta. 20Takan marabci talakawa takan kuma taimaki masu bukata. 30Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe; amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce. 31Ka ba ta ladar da ya dace tă samo wa kanta, bari kuma ayyukanta su kawo mata yabo a ƙofar shiga birni.
Zaburar amsawa
1Waƙar haurawa. Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa. 2Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka. 3Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya a cikin gidanka; ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka. 4Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji. 5Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima,
Karatu na biyu
1To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku, 2gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare. 3Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba. 4Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo. 5Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne. 6Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai.
Bishara
14“Har wa yau, za a kwatanta shi da mutumin da zai yi tafiya, wanda ya kira bayinsa ya kuma danƙa musu mallakarsa. 15Ga guda, ya ba shi talenti biyar na kuɗi, ga wani talenti biyu, ga wani kuma talenti ɗaya, kowa bisa ga azancinsa. Sa’an nan ya yi tafiyarsa. 16Mutumin da ya karɓi talenti biyar, nan da nan ya tafi ya yi kasuwanci da su har ya sami ribar talenti biyar. 17Haka ma, wannan mai talenti biyu, shi ma ya yi riba biyu. 18Amma mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ɗin, ya tafi, ya tona rami, ya ɓoye kuɗin maigidansa. 19“Bayan an daɗe, sai maigidan bayin nan ya dawo, ya kuma daidaita lissafi da su. 20Mutumin da ya karɓi talenti biyar, ya kawo ƙarin talenti biyar. Ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyar. Ga shi, na yi ribar biyar.’ 21“Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’ 22“Mutumin da yake da talenti biyu, shi ma ya zo ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyu; ga shi, na yi ribar biyu.’ 23“Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’ 24“Sa’an nan mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ya zo. Ya ce, ‘Maigida, na san cewa kai mutum ne mai wuyan sha’ani, kana girbi inda ba ka shuka ba, kana kuma tara inda ba ka yafa iri ba. 25Saboda haka na ji tsoro, na je na ɓoye talentinka a ƙasa. Ga abinka.’ 26“Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Kai mugun bawa, mai ƙyuya! Ashe, ka san cewa ina girbi inda ban yi shuka ba, ina kuma tarawa inda ban yafa iri ba? 27To, in haka ne, ai, da ka sa kuɗina a banki, don sa’ad da na dawo da na karɓi abina da riba. 28“ ‘Karɓi talentin daga hannunsa ku ba wanda yake da talenti goma. 29Gama duk mai abu za a ƙara masa, zai kuma same shi a yawalce. Duk wanda ba shi da shi kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa. 30Ku jefar da banzan bawan nan waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Albert Babba, bishop kuma malamin Ikkilisiya
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi A, shekarar ranakun mako II.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi