Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Nuwamba 2026 › Nuwamba 13
Kalandar Ortodoks · 31 ga Oktoba (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Nuwamba 13, 2026
Juma’a · Mako na 24 bayan Fentekos · Sauti na 6
Bukukuwa da waliyyai
Apostles of the 70: Stachias, Amplias, Urban, Narcissos, Apellias and Aristoboulos (1st C)
Ranar azumi
Azumi: da mai
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Wasiƙa
9Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi. 10Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi. 11Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi. 12To, muna roƙonku, ’yan’uwa, ku girmama waɗanda suke aiki sosai a cikinku, waɗanda suke bisanku cikin Ubangiji da kuma waɗanda suke yin muku gargaɗi. 13Ku riƙe su da mutunci sosai cikin ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna. 24Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata. 25’Yan’uwa, ku yi mana addu’a. 26Ku gaggai da dukan ’yan’uwa da sumba mai tsarki. 27Na gama ku da Ubangiji ku sa a karanta wannan wasiƙa ga dukan ’yan’uwa. 28Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku.
Bishara
23“Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni, wanda kuma ba ya tarawa da ni, watsarwa yake yi. 24“Lokacin da mugun ruhu ya fita daga mutum, sai ya bi ta wuraren da ba mutane, yana neman hutu, amma ya kāsa samu, sai ya ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ 25Sa’ad da ya koma, ya tarar da gidan a share da tsabta, kuma a shirye. 26Sai ya je ya ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, sai su shiga su zauna a wurin. Ƙarshen wannan mutum kuwa zai fi farkonsa muni.”
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Oktoba 31 a kalandar ikilisiya shi ne Nuwamba 13 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi