Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Nuwamba 2026 › Nuwamba 12
Kalandar Ortodoks · 30 ga Oktoba (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Nuwamba 12, 2026
Alhamis · Mako na 24 bayan Fentekos · Sauti na 6
Bukukuwa da waliyyai
Hieromartyr Zenobios, Bishop of Aegea, and his sister Zenobia in Cilicia († 285)
Azumi
Babu azumi
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Wasiƙa
1To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku, 2gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare. 3Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba. 4Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo. 5Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne. 6Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai. 7Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa. 8Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano.
Bishara
14Sa’ad da Yesu yake fitar da wani beben aljani daga wani mutum, da aljanin ya fita, sai mutumin wanda da bebe ne, ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki. 15Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Be’elzebub, sarkin aljanu ne, yake fitar da aljanu.” 16Waɗansu kuma suka gwada shi, ta wurin neman yă nuna musu wata alama daga sama. 17Yesu kuwa ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa, zai lalace, kuma gidan da yake gaba da kansa zai rushe. 18In Shaiɗan yana gāba da kansa, yaya mulkinsa zai tsaya? Ina faɗin haka domin kun ce, da ikon Be’elzebub nake fitar da aljanu. 19In da ikon Be’elzebub nake fitar da su, to, da ikon wa masu binku suke fitar da su? Saboda haka, za su zama alƙalanku ke nan. 20Amma in da ikon Allah ne ni nake fitar da aljanu, ashe, mulkin Allah ya zo muku ke nan. 21“Sa’ad da mutum mai ƙarfi, wanda yake da makamai yana gadin gidan kansa, an tsare lafiyar dukiyarsa ke nan. 22Amma in wani wanda ya fi shi ƙarfi, ya faɗa masa ya kuma sha ƙarfinsa, yakan ƙwace makaman da mutumin ke dogara da su, ya kuma rarraba ganima. 23“Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni, wanda kuma ba ya tarawa da ni, watsarwa yake yi.
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Oktoba 30 a kalandar ikilisiya shi ne Nuwamba 12 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi