Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Nuwamba 2026 › Nuwamba 10
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Nuwamba 10, 2026
Talata · Mako na 32 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Talata a mako na 32 na lokacin yau da kullum
Tunawa · Launin ibada: fari
Waliyyi Leo Babba, Fafaroma kuma malamin Ikkilisiya · Tunawa
Karatun yini
Karatu na farko
1Dole ka koyar da abin da yake bisa sahihiyar koyarwa. 2Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri. 3Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari. 4Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu, 5su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah. 6Haka kuma, ka ƙarfafa samari su zama masu kamunkai. 7Cikin kowane abu ka zama musu misali mai kyau ta wurin aikata abin da yake nagari. A cikin koyarwarka ka nuna mutunci da ƙwazo 8da kuma sahihanci cikin maganar da ba za a iya kushewa ba, domin masu gāba da kai su ji kunya, su kuma rasa wani mugun abin da za su faɗa game da mu. 11Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane. 12Yana koya mana mu ce, “A’a” ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani, 13yayinda muke sauraron begenmu mai albarka bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi, 14wanda ya ba da kansa dominmu don yă fanshe mu daga dukan mugunta yă kuma tsarkake wa kansa mutanen da suke nasa, waɗanda suke marmarin yin abin da yake nagari.
Zaburar amsawa
3Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri; yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya. 4Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji zai kuwa biya bukatun zuciyarka. 18Kwanakin marasa zarge suna sane ga Ubangiji, kuma gādonsu zai dawwama har abada. 23In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi, zai sa sawu su kahu; 27Ku juyo daga mugunta ku yi alheri; sa’an nan za ku zauna a ƙasar har abada. 29Masu adalci za su gāji ƙasar su kuma zauna a cikinta har abada.
Bishara
7“In ɗaya a cikinku yana da bawa, wanda yake masa noma, ko kiwon tumaki, da dawowar bawan daga gonar, ai, ba zai ce masa, ‘Ka zo nan, ka zauna, ka ci abinci ba’? 8Ashe, ba zai ce masa, ‘Ka shirya mini abincin yamma, ka shirya ka yi mini hidima domin in ci in sha, bayan haka kana iya ci, ka kuma sha ba’? 9Shin, zai gode wa bawan don yă yi aikin da aka ce ya yi ne? 10Haka ku ma, bayan kun yi duk abin da aka ce muku ku yi, ya kamata ku ce, ‘Mu bayi ne marasa cancanta, mun dai yi aikinmu ne kaɗai.’ ”
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Leo Babba, Fafaroma kuma malamin Ikkilisiya
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi A, shekarar ranakun mako II.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi