Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Nuwamba 2026 › Nuwamba 2
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Nuwamba 2, 2026
Litinin · Mako na 31 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Tunawa da dukan masu bangaskiya da suka rasu
Ambato · Launin ibada: shunayya
Karatun yini
Karatu na farko
17An hana ni salama; na manta da ko mene ne ake kira wadata. 18Saboda haka na ce, “Darajata ta ƙare da kuma duk abin da nake begen samu daga wurin Ubangiji.” 19Na tuna da azabata da kuma sintiri, da na yi ta yi da ɗacin rai. 20Na tuna su sosai, sai kuma na ji ba daɗi a raina. 21Duk da haka na tuna da wannan na kuma sa bege ga nan gaba. 22Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba; gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa. 23Sababbi ne kowace safiya; amincinka kuwa mai girma ne. 24Na ce wa kaina, “ Ubangiji shi ne nawa; saboda haka zan jira shi.” 25Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa, ga kuma wanda yake neman shi; 26yana da kyau ka jira shiru domin samun ceton Ubangiji.
Zaburar amsawa
8Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna. 10ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu. 13Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa, haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa; 14gama ya san yadda aka yi mu, ya tuna cewa mu ƙura ne. 15Game da mutum dai, kwanakinsa suna kamar ciyawa da suke haɓaka kamar fure a gona; 16iska kan hura a kansa sai ya ɓace ba a kuwa sāke tuna da inda dā yake. 17Amma daga madawwami zuwa madawwami ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa, adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu,
Karatu na biyu
51Ku saurara, in gaya muku wani asiri. Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, sai dai duk za a sauya kamanninmu 52farat ɗaya, cikin ƙyaftawar ido, da busan ƙaho na ƙarshe. Gama za a busa ƙaho, za a tā da matattu da jiki irin da ba ya ruɓewa, za a kuma sauya kamanninmu. 53Gama dole mai ruɓa yă maye wa mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma yă maye wa mai mutuwan nan. 54Sa’ad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, sa’an nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, “An haɗiye mutuwa cikin nasara.” 55“Ya ke mutuwa, ina nasararki? Ya ke mutuwa, ina dafinki?” 56Zunubi ne yake ba wa mutuwa dafi, Doka kuma take ba wa zunubi iko. 57Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
Bishara
ko: Yoh 12:23–26
25A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Ina yabonka, Uba, Ubangijin sama da ƙasa, gama ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. 26I, Uba, gama wannan shi ne abin da ka ji daɗin yi. 27“Dukan kome Ubana ya danƙa mini. Ba wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban, sai dai Ɗan da kuma waɗanda Ɗan ya so yă bayyana musu shi. 28“Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi A, shekarar ranakun mako II.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi