Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A hanyar zuwa Urushalima

Littattafan Bishara gefe da gefe · A hanyar zuwa Urushalima

Ka ɗauki gicciyenka

Mat 16:24–28 · Mar 8:34–38; 9:1 · Luk 9:23–27

Mattiyu

Mat 16:24–28

24Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni.

25Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.

26Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai bayar a bakin ransa?

27Gama Ɗan Mutum zai zo cikin ɗaukakar Ubansa, tare da mala’ikunsa, sa’an nan zai ba wa kowane mutum lada gwargwadon abin da ya yi.

28“Gaskiya nake gaya muku, akwai waɗansu da suke tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin mulkinsa.”

Markus

Mar 8:34–38; 9:1

8:34Sai ya kira taron wurinsa tare da almajiransa ya ce, “Duk wanda zai bi ni, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa yă bi ni.

8:35Domin duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, da kuma bishara, zai same shi.

8:36Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa?

8:37Ko kuma, me mutum zai bayar a musayar ransa?

8:38Duk wanda ya ji kunyata, da na kalmomina a wannan zamani na fasikanci da zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa lokacin da ya shiga cikin ɗaukakar Ubansa, tare da tsarkakan mala’iku.”

9:1Ya kuma ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.”

Luka

Luk 9:23–27

23Sai ya ce wa dukansu, “In wani zai bi ni, dole yă mūsanta kansa, ya ɗauki gicciyensa kowace rana, ya bi ni.

24Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni zai same shi.

25Ina amfani, in mutum ya ribato duniya duka, amma ya rasa ransa, ko kuma ya yi hasarar ransa.

26Duk wanda yake jin kunyana da na kalmomina, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa sa’ad da zai zo a cikin ɗaukakarsa, da ɗaukakar Uban, da kuma ta tsarkaka mala’ikun.

27“Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su ga mutuwa ba, sai sun ga mulkin Allah.”

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY