Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Disamba 2027 › Disamba 29
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Disamba 29, 2027
Laraba · Lokacin Kirsimeti
Bukukuwa da waliyyai
29 ga Disamba — rana ta biyar a cikin kwana takwas na Kirsimeti
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: fari
Waliyyi Thomas Becket, bishop kuma shahidi · Ambato
Karatun yini
Karatu na farko
3Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa. 4Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa. 5Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa. 6Duk wanda ya ce yana rayuwa a cikinsa dole yă yi tafiya kamar yadda Yesu ya yi. 7Abokaina ƙaunatattu, ba sabon umarni nake rubuta muku ba, a’a, daɗaɗɗen umarnin nan ne, wanda kuke da shi tun farko. Wannan tsohon umarni shi ne saƙon da kuka riga kuka ji. 8Duk da haka ina rubuta muku sabon umarni; ana ganin gaskiyar umarnin a cikinsa da kuma cikinku, gama duhu yana shuɗewa, haske na gaskiya kuwa yana haskakawa. 9Duk wanda ya ce yana cikin haske yana kuma ƙin ɗan’uwansa, ashe a duhu yake har yanzu. 10Duk wanda yake ƙaunar ɗan’uwansa, a cikin hasken yake rayuwa ke nan, kuma babu wani abin da yake cikinsa da zai sa yă yi tuntuɓe. 11Amma duk wanda yake ƙin ɗan’uwansa, cikin duhu yake, yana kuma tafiya cikin duhu ke nan; bai ma san inda za shi ba, domin duhun ya makanta shi.
Zaburar amsawa
1Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji; ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka. 2Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa; ku yi shelar cetonsa kowace rana. 3Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, manyan ayyukansa a cikin dukan mutane. 5Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ne ya yi sammai. 6Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa.
Bishara
22Da lokacin tsarkakewarsu bisa ga Dokar Musa ya cika, sai Yusuf da Maryamu suka ɗauke shi suka haura zuwa Urushalima don su miƙa shi ga Ubangiji 23(yadda yake a rubuce a Dokar Ubangiji cewa, “Kowane ɗan fari, za a keɓe shi ga Ubangiji”), 24don kuma su miƙa hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Dokar Ubangiji cewa, “kurciyoyi biyu ko ’yan tattabarai biyu.” 25To, akwai wani mutum a Urushalima mai suna Siman, shi mai adalci da kuma mai ibada. Yana jiran fansar Isra’ila, Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi. 26An bayyana masa ta wurin Ruhu Mai Tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kiristi na Ubangiji. 27Da Ruhu ya iza shi, sai ya shiga cikin filin haikali. Sa’ad da iyayen suka kawo jaririn nan Yesu don su yi masa abin da al’adar Doka ta bukaci, 28sai Siman ya karɓi yaron a hannuwansa ya yabi Allah, yana cewa, 29“Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kamar yadda ka yi alkawari, yanzu ka sallami bawanka lafiya. 30Gama idanuna sun ga cetonka, 31wanda ka shirya a gaban dukan mutane, 32haske don bayyanawa ga Al’ummai da kuma ɗaukaka ga mutanenka Isra’ila.” 33Mahaifin yaron da kuma mahaifiyarsa suka yi mamaki abin da aka faɗa game da shi. 34Sa’an nan Siman ya sa musu albarka ya ce wa Maryamu mahaifiyarsa, “An ƙaddara yaron nan yă zama sanadin fāɗuwa da tashin mutane da yawa a Isra’ila, zai kuma zama alamar da mutane ba za su so ba, 35ta haka za a fallasa tunanin zukatan mutane da yawa. Ke ma, takobi zai soki zuciyarki.”
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Thomas Becket, bishop kuma shahidi
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi C, shekarar ranakun mako II.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi