Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Disamba 2027 › Disamba 5

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Disamba 5, 2027

Lahadi · Mako na 2 na lokacin Zuwan Ubangiji

Bukukuwa da waliyyai

Lahadi ta 2 ta lokacin Zuwan Ubangiji

Lahadi · Launin ibada: shunayya

Karatun yini

Karatu na farko

Ba ya cikin wannan fassara

Zaburar amsawa

Zab 126:1–6

1Waƙar haurawa. Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona, mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki. 2Bakunanmu sun cika da dariya, harsunanmu da waƙoƙin farin ciki. Sai ana faɗi a cikin al’ummai, “ Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.” 3Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu, mun kuwa cika da farin ciki. 4Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji kamar rafuffuka a Negeb. 5Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki. 6Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna.

Karatu na biyu

Fil 1:4–6, 8–11

4A cikin dukan addu’o’ina dominku duka, nakan yi addu’a da farin ciki kullum 5saboda tarayyarku a cikin bishara daga ranar farko har yă zuwa yanzu, 6da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yă zuwa ranar Kiristi Yesu. 8Allah shi ne shaidata, ya san yadda nake ƙaunarku duka da ƙaunar Kiristi Yesu. 9Addu’ata ita ce ƙaunarku tă yi ta cin gaba da ƙaruwa cikin sani da kuma zurfin ganewa, 10don ku iya rarrabe abin da yake mafi kyau, ku kuma zama da tsarki, marasa aibi har yă zuwa ranar Kiristi, 11cikakku da sakamakon aikin adalci da yake zuwa ta wurin Yesu Kiristi, zuwa ga ɗaukakar Allah da kuma yabonsa.

Bishara

Luk 3:1–6

1A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tiberiyus, a lokacin Buntus Bilatus ne gwamnar Yahudiya, Hiridus kuma yana sarautar Galili, ɗan’uwansa Filibus yana sarautar Ituriya da Tarakunitis, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiline. 2A lokacin ne Annas da Kayifas suke manyan firistoci. Sai maganar Allah ta zo wa Yohanna, ɗan Zakariya a hamada. 3Ya zaga dukan ƙasar da take kewaye da Urdun, yana wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai. 4Kamar yadda yake a rubuce a littafin annabi Ishaya. “Muryar mai kira a hamada, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa. 5Za a cike kowane kwari, a farfashe kowane dutse da kowane tudu. Za a miƙe hanyoyin da suka karkace, a gyaggyara hanyoyi masu gargaɗa su zama sumul. 6Dukan ’yan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’ ”

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi C, shekarar ranakun mako II.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi