Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2027 › Oktoba 6
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Oktoba 6, 2027
Laraba · Mako na 27 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Laraba a mako na 27 na lokacin yau da kullum
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore
Waliyyi Bruno, firist · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
1Sai abin ya ɓata wa Yunana rai ƙwarai har ya yi fushi. 2Sai ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, ba irin abin da na faɗa ke nan ba tun ina gida? Wannan ne ya sa na yi ƙoƙarin tserewa zuwa Tarshish. Ai, na sani kai Allah ne mai alheri da tausayi, mai jinkirin fushi da cikakkiyar ƙauna, kai Allah ne mai dakatar da nufinka na yin hukunci. 3Yanzu, ya Ubangiji, ka ɗauki raina, domin ya fi sauƙi a gare ni in mutu da in rayu.” 4Amma Ubangiji ya amsa, ya ce; “Daidai ne ka yi fushi?” 5Sai Yunana ya fita daga birnin ya yi wajen gabas, ya zauna. A nan ya yi wa kansa rumfa, ya zauna cikin inuwarta yana jira yă ga abin da zai sami birnin. 6Sai Ubangiji Allah ya sa wata ’yar kuringa ta tsiro, ta yi girma a inda Yunana yake, don ta inuwantar da shi, yă ji daɗi. Yunana kuwa ya yi murna matuƙa da wannan kuringa. 7Amma kashegari da safe sai Allah ya sa tsutsa ta cinye ’yar kuringar har ta mutu. 8Sa’ad da rana ta yi sama, sai Allah ya sa iskar gabas mai zafi ta huro, zafin ranar kuma ya buga kan Yunana, har ya ji sai ka ce zai suma. Ya so a ce ya mutu ma, sai ya ce, “Gara in mutu da a ce ina zaune da rai.” 9Amma Allah ya ce wa Yunana, “Daidai ne ka yi fushi saboda wannan kuringa?” Sai Yunana ya ce, “I, daidai ne, ina fushi matuƙa, har ina so da na mutu ma.” 10Sai Ubangiji ya ce, “Ai, wannan kuringa ta tsira dare ɗaya ta kuma ɓace kafin dare na biyu, ba ka yi wata wahala dominta ba, ba kai ne ka sa ta yi girma ba, duk da haka ranka ya ɓace saboda ita. 11Ashe, ba dole ne in ji tausayin babban birnin nan Ninebe mai mutum sama da dubu ɗari da ashirin (120,000) marasa alhaki, da kuma dabbobi masu yawa ba?”
Zaburar amsawa
3Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama na yi kira gare ka dukan yini. 4Ka ba bawanka farin ciki gama gare ka, ya Ubangiji, na miƙa raina. 5Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji, cike da ƙauna ga dukan waɗanda suke kira gare ka. 6Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; ka saurari kukata na neman jinƙai. 9Dukan al’umman da ka yi za su zo su yi sujada a gabanka, ya Ubangiji; za su kawo ɗaukaka ga sunanka. 10Gama kai mai girma ne kana kuma aikata ayyuka masu banmamaki; kai kaɗai ne Allah.
Bishara
1Wata rana Yesu yana addu’a a wani wuri. Da ya gama, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Ubangiji, ka koya mana yin addu’a, kamar yadda Yohanna ya koya wa almajiransa.” 2Sai ya ce musu, “Sa’ad da kuke yin addu’a ku ce, “ ‘Ya Uba, sunanka mai tsarki ne mulkinka ya zo. 3Ka ba mu kowace rana abincin yini. 4Ka gafarta mana zunubanmu, kamar yadda mu ma ke gafarta wa duk wanda ya yi mana laifi. Kada ka bari a kai mu cikin jarraba.’ ”
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Bruno, firist
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi